Assalamu alaikum uwar gida yau na kawo muku hanyan da zaku bi Ku ajiye timatir din ku har sama Da wata Guda ba tare da ya lalace ba. Da fark...
Assalamu alaikum uwar gida yau na kawo muku hanyan da zaku bi Ku ajiye timatir din ku har sama Da wata Guda ba tare da ya lalace ba.
Da farko zaki Wanke timatir din ki, sae Ki zafasa shi Amma Ki saka gishiri a tafashen, zaki tafasa shi kaman na minti uku, sae Ki sauke Ki Wanke Ki markade shi Amma da kauri Kar yayi ruwa, to bayan kin markada sae Ki nemi mayar Da shi Wuta Ki tafasa markaden Shima ya dafu, sae Ki sauke Ki nemi kwalba mae kyau ki juye a ciki, idan kun juye sae Ki saka shi a ruwa tafasheshshe su Kara tafasuwa tare na Kamar na minti uku, idan kun sauke shknan, zaki iya ajiye shi duk inda kika ga dama har sama Da wata daya ba tare da ya lalace ba.
COMMENTS