Kuraren da iyaye ke tafkawa yayin shayar Da jarirai a wata shidan farko sun hada da 1. Rashin saka wa yaro nono gaba daya a bakin sa, Hakan...
Kuraren da iyaye ke tafkawa yayin shayar Da jarirai a wata shidan farko sun hada da
1. Rashin saka wa yaro nono gaba daya a bakin sa, Hakan yakan haifar da kumburin ciki wa jariran domin iska yana shiga ta yanda nonon bai gama shiga ba.
2. Canjawa yaro nono, bincike ya nuna Cewa idan yaro ya Fara shan nono Da farko ruwa ne ke zuwa kafun nonon ya biyo baya, kin ga bayan ya gama zuqe ruwan nono na farko kafun ya Fara shan aenihin nonon Kuma kin Kara canja mishi wani, kin ga sae sha ruwa Sau biyu kenan kuma cikin shi sae ya cika da ruwa kawae Wanda Hakan zae jawo rama ga jariri.
3. Bawa jariri ruwa kafun wata shida, nonon uwa 80% nashi ruwa ne, kin ga kenan Hakan zae iya haifar Da rama ga jaririn.
MUHIMMANCIN SHAYAR DA JARIRI NONO ZALLA KAFUN WATA SHIDA
1. Yana Kara musu basira
2. Yakan zamo musu garkuwa a jikin su
3. Kare su daga cututtuka
4. Kara shakuwa da uwa.
COMMENTS