"Na san waye Buhari, kuma shi ma yasan koni waye. Daga nan har ranar da zan mutu Buhari zai cigaba da kira na da kalmar Sir (maigida) ...
"Na san waye Buhari, kuma shi ma yasan koni waye. Daga nan har ranar da zan mutu Buhari zai cigaba da kira na da kalmar Sir (maigida) "A shekarar 2015 da Buhari ya tsaya takarar shugaban kasa, idan da ban goyi bayansa, ba yadda zai yi yaci zabe. "Saboda haka ina da damar na ci gyaransa saboda bai kamata a ce Nijeriya tana cikin yanayin da take ciki ba a yanzu. "Ya kamata a ce Nijeriya ta wuce inda take yanzu, saboda Allah ya hore mana dukkanin wani abu da zai ba mu damar cigaba. "Na cancanci na yi magana akan Buhari kuma na kalubalance shi. Na farko dai nayi abinda ya dace domin na kalubalance shi a inda naga akwai matsala. Na biyu kuma na bada jinina domin wannan kasar tamu, kai har d'ana na ciki na shi ma ya bada jininsa akan cigaban wannan kasar, saboda haka me zai hana na yi magana akan abin da zai kawo cigaban wannan kasar? Saboda nama wuce cancanta indai akan magana ne akan abinda ya shafi kasar nan"

COMMENTS