Blog Archive

Powered by Blogger.

NASAN MASU MIN FATAN MUTUWA A LOKACIN DA NAYI ZAMAN JINYA A LONDO - inji SHUGABA BUHARI

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce mutane da dama sun yi masa fatan mutuwa a lokacin da yake jinya a 2017. Shugaban ya bayyana haka ...

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce mutane da dama sun yi masa fatan mutuwa a lokacin da yake jinya a 2017. Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya ke ganawa da 'yan Najeriya mazauna Poland, a ziyarar da ya kai kasar domin halartar taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya. Ya ce wasu masu yi masa wanna "mugun fatan na mutuwa" har sun fara neman mukamin mataimakin shugaban kasa, idan Osinbajo ya zama shugaban kasa. "Mutane da dama sun dauka cewa zan mutu a lokacin da na yi rashin lafiya. Wasu daga cikin su sun rika zuwa wurin mataimakin shugaban kasa suna kamun kafa domin ya ba su mukamin mataimakin shugaban kasa saboda sun dauka na riga na mutu," in ji Buhari. Ya ce "amma mutumin ya ji kunya, kuma har ma ya ziyarce ni a London lokacin da na ke samun sauki." Buhari dai na fadar haka ne lokacin da ya ke amsa tambayar wani dan Najeriya da ya tambaye shi ko shi ne Buharin ainihi na Daura ko kuwa wani ne aka kawo daga Sudan ya ke kwaikwayonsa? Wasu 'yan kasar dai musamman a yankin kudancin kasar na yada jita-jitar cewa Buhari na Najeriya ya jima da mutuwa, don haka wani ne yake kwaikwayonsa, ana yi wa 'yan Najeriya "angulu da kan zabo." To sai dai a amsar da ya bayar Buhari ya ce "ni ne na ainihi, ina tabbatar muku da haka. Kuma nan ba da jimawa ba zan yi bikin cikar shekara 76 a duniya, kuma zan kara karfi. Shugaban ya soki masu yada wannan jita-jita, inda ya ce "ba su san ya kamata ba, kuma abu ne da ya sabawa koyarwar duk wani addini". Wannan ne karon farko da shugaba Buhari da gwamnatinsa ke maida martani kan kalaman da ake yi cewa ba Buhari na ainihi ne ke mulkin Najeriya ba.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: NASAN MASU MIN FATAN MUTUWA A LOKACIN DA NAYI ZAMAN JINYA A LONDO - inji SHUGABA BUHARI
NASAN MASU MIN FATAN MUTUWA A LOKACIN DA NAYI ZAMAN JINYA A LONDO - inji SHUGABA BUHARI
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiEdgY0YWigjTlfTyfJaRAi33Dwi0ItvmQUW-qMdtIIuEzuc9ki1qvk3s8jHwQFUWB6nNwxqCRGdojKQSBuxGBafMGrifZgjQJD9fdygKe_eoPMTGv0fe1-2M8UytoC59y-cmZ0bKiiO3pq/s320/Buhari-2.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiEdgY0YWigjTlfTyfJaRAi33Dwi0ItvmQUW-qMdtIIuEzuc9ki1qvk3s8jHwQFUWB6nNwxqCRGdojKQSBuxGBafMGrifZgjQJD9fdygKe_eoPMTGv0fe1-2M8UytoC59y-cmZ0bKiiO3pq/s72-c/Buhari-2.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/12/nasan-masu-min-fatan-mutuwa-lokacin-da.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/12/nasan-masu-min-fatan-mutuwa-lokacin-da.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy