Hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun kai mamaya gidan da ýaýan Atiku Abubakar biyu ke zama a Abuja a karshen mako, jaridar Premium Times...
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa sun kai mamaya gidan da ýaýan Atiku Abubakar biyu ke zama a Abuja a karshen mako, jaridar Premium Times ta ruwaito. Haka zalika Chimeka Orji, dan tsohon gwamnan jihar Abia, Theodore Orji na zama ne a gidan. An kuma rahoto cewa jami’an hukumar yaki da rashawan sun binciki sashinsa. Koda dai majiyoyi sun bayyana cewa gidan ýaýan Atiku ne musababbin zuwansu, wani kakakin hukumar yaki da rashawar ya bayyana cewa babu mamaki saoda Chiemeka suka kai mamayar. Mamayar da aka kai gidan Aliyu Da Mustapha Atiku Abubakar a Maitama a ranar Asabar na zuwa ne kwana guda bayan hukumomin tarayya sun daskarar da asusun abokin takarar Atiku, Peter Obi. Hukumomin yaki da rasha biyu EFCC da ICPC sun karyata daskarar da asusun bankin Obi. Paul Ibe, kakakin iyalan Atiku Abubakar, ya tabbatar da binciken a ranar Lahadi, cewa jami’an da suka gudanar da “lamarin mai cike da barazana basu samu komai ba

COMMENTS