Blog Archive

Powered by Blogger.

[Hausa Novel] MIJIN MARAINIYA PART 1

[Hausa Novel] MIJIN MARAINIYA PART 1 . . Na Fadeela Lamido . Bismillahir rahmanir rahim . Zaune take a dan ma tsakaicin gidan su tana ta fam...

[Hausa Novel]
MIJIN MARAINIYA PART 1
.

.
Na Fadeela Lamido
.
Bismillahir rahmanir rahim
.
Zaune take a dan ma tsakaicin gidan su tana ta
faman share hawaye wata dattijuwan mata ce ta fito daga daki tana fadin , kin fara ko, dama ke idan
tsohon munafunci ki ya tashi ba mutunci gareki ba,
wlh uwarki ta bar miki mugun gado, ki zauna kiyi
ta kuka salon iya ta ce ana miki wani abu, matsuwa
tayi ta rike mata kunne tace ai baki ga komai ba
safna sai rada na koreki gidan nan , zakiyi kuka, yadda uwar ki tasani kuka ta tura min bakin ciki
kema sai na tura miki bakin cikin da zai kashe ki .
Safna taji zafin wannan ruko, fitsari ne yake bin
kafafun ta, tace goggo dan allah kiyi hakuri , indai
kuka ne na daina. Kar ma ki daina dan jakar
ubanki, tashi maza ki wanke kafafunki ki dauki rake , kuma karki dawo gidan nan sai ya kare. Jiki
na rawa safna ta mike ta dauki bukiti taja ruwa a
rijiya ta shiga bayi, cikin sauri safna ke wanka dan
gudun fadan goggo. goggo na tsaye safna ta fito
da bukitin wanka a hannun ta goggo ta bita da
harara , da sauri tashiga dakin ma haifiyar ta, wanda a yanzun ita kadai take kwana acikin sa,
cikin sauri ta jawo ledan kayan ta, ta fara cirowa
tana dubawa duk tsun mukara ne , masu dan kyan
goggo ta kwashe tayi kyauta dasu, haka dai ta
dauki daya daga ciki ta saka, tadauki raken goggo
ta kama hanya. tafe take tana hada hanya domi ita bata iya tallah ba sai dai idan mutun ne yakira ta
,haka tai ta tafiya ko nera ba tayi ba, ta gaji ta koma
gida. goggo na zaune a tabarma ita da yaran ta
guda biyu iro da salma, safna ta shigo , goggo ta
mike yanzun nan dawo min da raken nan kikayi ,
iro tashi kaba yarinyar nan kashi rashin duka ke damun ta. Kamar jira yake yamike da sauri ya fara
kai mata duka daga kar she ma dukkan su suka
taron mata wannan na duka wannan nayi , sai da
suka ga bata iya motsi suka bar ta
.
WAIWAYE malam musa mutumin kirki ne matan sa biyu
goggo itace uwar gida, sai mahaifiyar safna wanda
suke kira Inna, tunda malam musa ya auri goggo ta
haifi iro bata kara haihuwa ba dan haka iya
mahaifiyar malam musa ta matsamai ya kara aure,
duk inda malam musa yaje neman aure ba a bashi saboda masifar matar shi, wata rana malam musa
na cikin tafiya akan tsuhuwar mashin dinsa yaci
karo da wata bafulatana batafi shekara sha biyar
ba tana tafiya tana kuka, tsayawa yayi ya tam baye
ta lfy take kuka, sai da ta share hawaye sannan
tace wata yaya tace tayi aure a binni tunda mijin ya tafi da ita har yau bamu sake ganin ta ba, shine
muka fito neman ta su baffah suka ce na jira su
karkashin wata bishiya tunjiya har yanzun basu
dawo ba, malam yace ina ne garinku , kame kame
takama malam dai yagane bata san sunan garin su
ba, goya ta yayi abayan mashin din sa dan su kara duba wajan ko iyayan ta sun dawo, suna zuwa
suka duba babu kowa awajan , dan haka malam
musa yace ma wani abukin sa dake zaune a waja
bayanin cewa ko da iyayan ta sun dawo ya kawo
su gidan shi. malam musa gidan iya ya wuce da yar
fillo saudatu dan yasan halin matar sa, iya ta kar beta hannu biyu tare da mamakin wauta irin na
filani, sai da saudatu tayi shekara biyu awajan iya
ba labarin iyayan ta ,dan haka iya ta matsawa
malam musa ya auri saudatu, malam musa yabi
umarnin ma haifiyar shi dan shima yafara tunanin
haka. bayan an daura musu aure da wata uku goggo ta sake haihuwan salma itako amarya
saudatu sai da ta shekara biyu sannan ta haifi safna
, saudatu tasha wahala a gun goggo dan ma tana
samun kariya agun malam safna nada shekara sha
hudu tafiya ta kama malam zuwa kauyen su iya
dan kai masu ziyara, iya tace atafi da saudatu tunda bata taba zuwa ba. lokacin safna nazuwa
makarantar primary tana aji shidda dan haka suka
barta gun goggo, bayan wani dan lokaci da tafiyan
su labari ya same su, motar da suka shiga ta kone
kurmus babu wanda yayi rai, haka su kai ta kuka a
yanzun haka shekaran su daya da rasuwa inda goggo tahana safna makaranta sai tallan rake.
.
Abduljalal wani matshin yaro ne me ji da kanshi
daka ganshi kaga dan gata bazai wuce shekara
ashirin da bakwai ba, dogo ne sosai yanayin
tsawan shi sai ka zaci ya wuce shekarun shi haka fari ne tas, bashi da yawan fara,a. Idan kaga jalal na
dariya to da ummin sa ne , ko kuma cikin abokan
sa, zuwa yayi ya samu ummin sa zaune a falo, yaje
ya fada jikin ta yana fadin ummi yinwa nake ji.
ummi tace jalal karfa ka karya ni, wai kai baka san
ka girma bane. haba ummi wanni girma nayi ne, kodan kinga kin samu wata.
.
tace ba haka bane jalal ya kamata ka fahimci cewa
ka girma yanxun fan ba da bane, ga abinci nan
kaci , karani gida hajiya sahura. cokali daya ya kai
bakin sa yace ummi na gaji zo ki bani abaki. gargiza kai ummi tayi ta matso ta fara bashi abaki sai da ya
koshi yace ummi bar shi haka na koshi. sai da
ummi ta shiga ta gama gyara wa sannan ta fito, ta
samu jalal na zaune a falo kanan kaya ne a jikin shi
yayi kyau sosai, idan kaga jalal da ummin sa sai ka
rantse yayar sa ce, jalal ne ke jan motan ba, suna tafiya suna hira . sunyi nisa sosai sun shiga
unguwan su hajiya saratu abduljalal ya hango wata
yarinya tana tafe tana kuka ga kuma rake akan ta,
yace ummi ji wata yarinya yar karama an daura
mata talla, yanzu dan Allah ummi wa zai sha
wannan raken kofa kan kare shi ba,ayi ba. ummi tace kai kake ganin haka jalal kazamai yan uwan ta
zasu sha. jalal na kawowa kusa da yarinyar ya
tsaya ya kira ta da gudu ta karaso, yace me yasa
meki kike kuka? tace idan na koma gida raken nan
be kare ba duka, duka za,ayi min, jalal ya tausaya
mata ya kalli jikin ta yaga shedan bulala, yace ummi zan saya raken nan. da sauri ummi tace amman dai
ba a mota ta zaka zuba wannan kazamin raken ba.
yace sai ta bawa almajirai , ya sunan ki ya tam baye
tace safna sai da ya maimaita sunan sannan yace
raken na nawa ne? tace nera dari, dari biyu ya ciro
ya mika mata, tamiko hannu zata karba , ummi ta daka mata tsawa taja baya da sauri, jalal yace ummi
me tayi ? yaro ban yadda ku hada hannun da
yarinyar nan ba ka aje mata akasa sai ta dauka.
.
Jalal yace haba ummi ai ba taba ta zanyi ba, bata
kawai zan yi. ummi tace ashe tsaftar ka ta banza ce , idai ka bawa yarinyar nan da hannun ka kuwa.
juyawa yayi ya ajewa safna kudin akasa, da saurin
ta ta tsuguna ta dauka tana ma jalal godiya, ummi
ko hararar ta kawai take. bayan sun dawo gida
ummi ta lura jalal fushi yake da ita, dan haka ta
bishj har dakin sa, tace jalal me ya same ka, kake ta fushi? abduljalal be iya boye wa ummi komai dan
haka yace ummi yarinyar nan ce take bani tausayi,
ummi da,a kwai yadda zanyi dana tai make ta.
ummi hada rai tayi tace yaro halin ka yana bani
mamaki in banda abinka ina ruwan ka da yayan
talakawa da har zaka damu kan ka, akan wata banza yarinya kazama, da kikiya. ummi bazaki
gane ba nasan da dady ne zai fahimce ni, ummi
raken nera dari ne fa akanta, ummi kuma gashi
yarinyar kyakyawa da ita. zoro ido ummi tayi tace
yaro kai ne kuwa, kaga yarinya mumuna kace
kyakyawa ko dai gamu kayi ne, to naji kyakyawa ce me kake nufi yan zon. ummi ni ba abinda nake
nufi kawai dai inason ki tai maka mata ne. kaga
jalal karna kuma jin manar yarinyar nan abakin ka,
ta mike da sauri tabar wajan. itako safna zuwa tayi
gurin wasu almajirai tana raba musu, iya na daga
gefe tana kallon safna, saida ta gama ta juya zata tafi iya ta kwala mata kira , ai tana ganin iya ta roga
da gudu ta kamkame ta, cikin rudu iya ta daga kan
safna tace a ina kika samu rake kike rabawa
Jama,a? Safna ta kwashe labari kaf ta fadawa iya,
salati iya ta shiga yi, tana fadin ina can zaune za,a
lalata min jika, wanne dan iskan ne, yabaki kudi? iya nima ban san shi ba kawai gannin su nayi
amota. be miki komai ba dai ko?
.
ba abinda yayi min, iya tasa keyar safna tayi tace
muje na samu goggon taki, in kaskiya ne ta
daurawa salma mana. suna shiga iya ta fara fada taita fada tundaga ranar rokon safna yadawo
hannun iya, safna dadi takeji sosai agurin iya babu
ta kura, iya duk ta. hada dan kudin da take da shi
ta mai da safna makaran ta, haka iya tai ta wahala
da safna ana haka safna ta gama primary schools,
gashi iya nason safna ta ci gaba da karatu kuma bata da kudi Dan haka ta fara toya kosai a kofar
gida, iya bata barin safna tazo gurin tuyan kosan ta
sai dai aikace aikacen cikin gida duk da cewa iya ba
wani karfi gareta ba, amman safna ta murje tayi
kyau kamar ba ita ba. a yanzun safna tana J S2 dan
haka iya ta fara tunanin aurar da safna dan duk da cewa safna bata wuce sha bakwai ba, itako safna
babban burin ta shine ta tayi karatu me zurfi. ana
cikin haka rashin lafyya ya kama iya dan kosan da
take yi ya gagara, safna ta rasa ya zatayi , tana kuka
ta nufi gidan goggo, ta gaya mata iya babu lafiya.
fada ta fara tana fadin aiga irin ta nan, kina nan muna neman kudi tazo ta dau ke ki, sai yanzun da
ciwo yakama zaki taho to bamu da kudi, wacce ki
bani waje karna kara ganin ki gidan nan, haka
safna ta juya tana tafe tana kuka. haka safna ta
dawo ta samu iya kwance cikin amai, ta shiga gyara
wajan bayan ta gama ta fara tunani yadda zata samo ma iya abincin da zata ci, tashi tayi ta fita ta
gama bulayin ta bata somo komai ba ba yadda
zatayi dole ta koma wurin goggo sai da ta gama
zagin ta sannan ta bata ragowar tuwan jiya da sauri
ta nufi gida tana ta sauri , tun kafin ta isa kofar
gidan ta hango muta ne tana shiga gidan kara kamkame tuwan ta tayi ta sheka da gudu tana
shiga taga an lulube ta da zani, safna fadawa tayi
jikin ta tana kuka. Wata makociyar su iya ta taho ta
dafa safna tace kiyi hakuri safna ki daina mata
kuka Allah ya karbi abinsa kuma ya fimu santa dan
haka sai muraka ta da.ardu,a haka safana taita kuka har aka kai iya makwanci ta safna bata bar
kuka ba. bayan anyi bakwai da yamma goggo ta
hada kayan ta ko salama batawa safna ba ta wuce
gida, gidan iya kuwa safna ce ka dai aciki sai ta
tsince kanta cikin matsanan cin tashin hankali,
haka safna ta kwana ita kadai acikin gidan, safna na tashi hankalin ta kara tashi yayi musamman da
ta leka dakin iya taga wayam dan haka ta tsoguna
abakin kofar iya ta saki Kara. makociyar iya baba
dije taji kukan safna aguje ta zagawo tace Ina
goggonki . safna tace ta tafi tunjiya au yanzu nan
nufinta baza ta rike kiba, lalai abin nata babba ne, tashi ki hada kayanki na rakaki .
.
cikin tashin hankali safna ke hada kayan ta tana
ganin ita meye amfanin ta tuda ba iyayen ta iyar ma
da take takama da ita ta tafi ta bar ta itama da
mutuwar kawai tayi. suna shiga gidan goggo suka same ta tana tankadan garin tuwo, tana ganin
safna ta hada rai, bayan sun gaisa tace yazaki tafi
kibar yarinya ita daya acin gida. cin sauri goggo ta
fara rantse rantsan ita sam bazata rike safna, baba
dije ta fahimci da gaske ta keyi tace to naji to me zai
hana ki kaita gun dangin iya. cinkin sauri goggo tace ina naga kudin motan da zan kai ta. kwance
haban zanin ta tayi takwaso gudin wajan duk ta
mikawa goggo ta sannu ta karba harda fadin
yauyau zan kai ta. goggo bata tashi kai safna ba sai
gaf da mangariba tace dauko kayanki mutafi ,
safna ta dauki kullin kayanta suka kama hanya, motar cikin gari suka hau , safna tace azuciyar ta
dama motar garin su iya acikin gari ake hawa ,take
farin ciki ya rufeta ko banza yau zataga gidaje masu
dan banan kyau . suna isa aka sauke su garin
kamar rana saboda fitilun da suke haka ko,ina
gidaje kuwa fadan kyansu bata lokaci. suna ta tafiya taki karewa ita dai safna bin goggo kawai
take suna zuwa gurin wata katuwar bishiya, goggo
tace safna zoki zauna anan naje na dawo , haka
banzayen kakannin ki sukama uwarki har ta mutu
bata kara saka su a idon taba.
.
Mijin marainiya2 loading....
.
comment and like for more:-

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: [Hausa Novel] MIJIN MARAINIYA PART 1
[Hausa Novel] MIJIN MARAINIYA PART 1
/img/702076/702076208_22b2781b0e.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2017/04/hausa-novel-mijin-marainiya-part-1.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2017/04/hausa-novel-mijin-marainiya-part-1.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy