Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ganin ya kare mutuncin ‘yan Nijeriya tare da kiyaye yardar da suka mika masa a koyaushe. Shug...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ganin ya kare mutuncin ‘yan Nijeriya tare da kiyaye yardar da suka mika masa a koyaushe. Shugaban ya bayyana hakan ne a yau Laraba a lokacin yakin neman zabensa a karo na biyu da ya gudana a garin Sakkwato. Ya ci gaba da cewa; gwamnatinsa ta samu nasara a bangarori Uku, wanda ya hada da yaki da cin hanci da rashawa, bunkasa sha’anin noma, da kuma bangaren tsaron kasarnan. Buhari ya ce; “Mun yi nasarar yaki da Boko Haram, bangaren noman mu ya samu gagarumin ci gaba, sannan a bangaren yaki da rashawa mun yi kokarinmu. Ina so na tabbatar muku da cewa; jam’iyyarmu zata ci gaba da amfani da alkibla mai kyau wajen ta kare mutunci ‘yan Nijeriya da kasarmu baki daya.” Inji shugaban kasar. shugaban kasar ya godewa al’ummar jihar Sakkwato bisa yadda suka fito domin tarbarsa a jihar. Jigo a jam’iyyar APC din, Bola Tinubu, ya tabbatarwa da ‘yan Nijeriya cewa; kasarnan zata ci gaba da kasance cikin zaman lafiya idan har shugaban kasa ya sake dawo wa a matsayin shugaban kasa. Ya ci gaba da cewa; ‘yan Nijeriya za su tudada domin ganin sun sake zabar jam’iyyar APC domin ci gaban kasarnan. Ciyaman din jam’iyyar Jihar, Sadiq Achida, ya tabbatar da cewa; al’ummar jihar za su zabi dukkanin ‘yan takararsu ne a zaben da za a yi.


COMMENTS