Ciwon hanta na nuna Wasu Alamu na Cewa an kamu Da cutar hanta. Kuma abinda ya kamata mutum ya Yi da zarar ya ga wadannan Alamu shine ya gagg...
Ciwon hanta na nuna Wasu Alamu na Cewa an kamu Da cutar hanta. Kuma abinda ya kamata mutum ya Yi da zarar ya ga wadannan Alamu shine ya gaggauta zuwa ga likita don a tabbatar masa da me ke damun shi tare Kuma da kokarin magance matsalar cikin gaggawa Kafun ta kae matsayin da hantar ba zata iya dawowa hayyacinta ba,
Kadan daga alamomin sune
1. Kumburin ciki musamman daga kasan Mara zuwa sama.
2. Yawaita yin Amai
3. Yin habo a kai a kai da Saurin fashewan fata ma'ana yin rauni
4. Kasala da Saurin gajiya
5. Rashin son cin abinci
6. Sauyawar launin idanu zuwa rawaya da Sauyawar launin fata.
7. Yawaita ciwon Mara.
8. Yawaita mantuwa, Rashin nutsuwa da Yawan damuwa.
Duk Wanda yaji wadannan alamomin dama Wasun su ya je domin yin gwajin cutar hanta.
COMMENTS