Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashi cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba wajen sawa al’umman kasar daga wurare daban-daban da suka...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashi cewa ba zai ba yan Najeriya kunya ba wajen sawa al’umman kasar daga wurare daban-daban da suka bashi yardarsu. Shugaban kasar yayi Magana ne a ranar Alhamis, 3 ga watan Janairu a fadar shugaban kasa da ke Abuja a wajen taron karramawa na kafofin watsa labaran Najeriya wato Nigerian Media Merit Award wanda kwamitin amintattu na kungiyar karrama kafofin watsa labarai ta shirya. Buhari Ya yabawa kokarin kungiyar sannan ya kara da cewa dama chan ya san mambobin kungiyar NMMA da dama tun ma kan ya san cewa zai kasance a wurin. Tsohon Darakta Janar na gidan talbijin din Najeriya (NTA), Mista Vincent Maduka wanda ya jagoranci tawagar yace Buhari ya cancanci zama zakaran shekara “saboda kana mutunta hakkin kafofin watsa labarai ba tare da kowani shamaki ba”. Ya bayyana cewa a karkashin Buhari babu kafar watsa labaran da aka rufe, sannan kuma an bayar da lasisin talbijin din makaranta na farko ga jami’ar Lagas, karkashin jagorancin shahararren malamin bangaren karatun jarida, Farfesa Ralph Akinfeleye.


COMMENTS