Shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su kauracewa zaben dan takarar shugaban kasa karkashi...
Shugaban jam'iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su kauracewa zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar inda ya ce zai sayar da Nijeriya in aka zabe shi a matsayin shugaban kasa. Oshiomhole yakara da cewa PDP ce silar matsin tattaalin arzikin da 'yan kasa ke ciki dan haka kada su kuskura su sake zaben jam'iyyar a yayin zaben shugaban kasa da zai guduna a ranar 16 watan Feburarun 2019. Oshiomhole ya fadi hakan ne a shekaran jiya Juma'a a yayin taron kaddamar da yakin neman zaben Gwmnan jihar Filato wato Simon Lalong a karo na biyu da ya gudana a filin wasan mosta jiki na garin Rwang Pam dake Jihar ta Filato.

COMMENTS