Shugaban kasar Nigeria, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa,gwamnatinshi bata da kudin da zata rika rabawa mutan maimakon haka zata yi amfani d...
Shugaban kasar Nigeria, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa,gwamnatinshi bata da kudin da zata rika rabawa mutan maimakon haka zata yi amfani da kudinne wajan yin ayyukan raya kasa. Buhari ya bayyana hakane jiya, Litinin wajan taron karawa jun sani da jam'iyyar APC ta shiryawa membobinta akan yanda zasu watsa manufofinta ga masu zabe. Shugaban ya bayyana cewa, zasu yi amfani da kudin gwamnatine wajan yin ayyukan raya kasa irinsu, tituna, tituna jirgin kasa dadai sauransu dan haka ya bukaci wadanda suka samu horaswa a taron da su je su jawo hankalin 'yan Najeriy da su zabi APC tare da gayamusu muhimmancin kuri'arsu. Shugaban ya kara da cewa a kullun rana ta Allah da Tunanin Najeriya da al'ummarta yake kwana yake tashi.

COMMENTS