Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zargi ‘yan siyasa da amfani da rikicin manoma da makiyaya domin cimma burinsu. Shugaba Buhari ya yi wannan...
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya zargi ‘yan siyasa da amfani da rikicin manoma da makiyaya domin cimma burinsu. Shugaba Buhari ya yi wannan bayanin ne a ranar Litinin bayan da aka samu barkewar rikici inda aka kashe wasu mutane sannan daga baya aka kai harin ramuwar gayya a Jos, Jihar Filato. A cewar Shugaban Kasa Buhari, kamar yadda babban mai taimaka masa a kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya sanar, “wasu mutane suna so su kawo rikici da rashin zaman lafiya wanda a tunaninsu zai taimaka musu wajen samun nasara a zaben 2019. “mun san cewa matsalar wajen zama da tattalin arziki na taimakawa wajen rura wutar rikicin da ke tsakananin manoma da makiyaya, amma kuma mun san cewa akwai ‘yan siyasa da suke amfani da rikicin domin cimma burinsu. Wannan ba karamin abin takaici bane,” inji shugaba Buhari.
COMMENTS