Blog Archive

Powered by Blogger.

Fursunoni guda 180 sun tsere daga gidan yari a jihar Neja

Wasu fursunoni da dama sun tsere daga gidan yari a Minna baban birnin jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya. Hukumar gidan yarin jihar...


Wasu fursunoni da dama sun tsere daga gidan
yari a Minna baban birnin jihar Neja da ke
arewa ta tsakiyar Najeriya. Hukumar gidan yarin jihar ta ce al'amarin ya faru ne
a ranar Lahadi da misalin karfe takwas na dare, a
gidan yarin mai matsakaicin tsaro da ke yankin
Tunga. Sanarwar da hukumar ta aike wa manema labarai
ta ce wasu 'yan bindiga dadi ne suka kai hari gidan
yarin inda suka yi ta musayar wuta da masu gadin
wajen, har suka samu damar shiga. Kawo yanzu an sake kama 30 daga cikinsu, yayin
da ake ci gaba da neman 180. Al'amarin ya jawo mutuwar wani ma'aikacin gidan
yarin daya da kuma dan acabar da ya dauko shi, a
yayin da suke daf da shiga gidan yarin, inda
ma'aikacin zai shiga aikin dare.Ministan harkokin cikin gida na kasar
Abdulrahman Bello Dambazau ya isa garin na
Minna don ganin irin barnar da lamarin ya jawo. Sanarwar ta ce a yanzu hankula sun kwanta kuma
hukumomin tsaro na ci gaba da "aiki ka'in da na'in
don tabbatar da cewa an kamo dukkan wadanda
suka tsere." Kafar watsa labarai ta PR Nigeria ta ruwaito Minista
Dambazau yana cewa gwamnatin tarayyar Najeriya
na gina gidan yari mai daukar mutum 3000 a ko
wacce shiyya ta kasar, za kuma a dauki ma'aikata
6000, amma ya tabbatar da cewa akwai karancin
tsaro a gidan yarin na Minna. "Akwai matsalar rashin tsaro da ya kamata a
shawo kanta a gidajen yari kamar rashin isassun
ma'aikata da kuma cunkoso," in ji minsitan a cewar
PR Nigeria.
.
Source @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Fursunoni guda 180 sun tsere daga gidan yari a jihar Neja
Fursunoni guda 180 sun tsere daga gidan yari a jihar Neja
https://ichef.bbci.co.uk/news/320/cpsprodpb/54AC/production/_101867612_f8493980-c588-4e45-88c4-37f522f88123.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/fursunoni-guda-180-sun-tsere-daga-gidan.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/fursunoni-guda-180-sun-tsere-daga-gidan.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy