Babban Kotun Jihar Kaduna ta daya da ke Zariya, ta yake wa wani tsoho da ake zargin ya dade yana bata yara ’yan firamare ’yan kasa da shekar...

Babban Kotun Jihar Kaduna ta daya da ke Zariya, ta
yake wa wani tsoho da ake zargin ya dade yana
bata yara ’yan firamare ’yan kasa da shekara
bakwai daurin rai-da-rai. Tsohon mai suna Husaini Abdu wanda aka fi sani
da Husaini dan Daura mai kimanin shekara 70 yana
sana’ar tsibbu ne da buga bulo, kuma yana zaune
da iyalinsa a gidan marigayi Habun Kakke da ke
Layin Makarantar Shehu Sifili a Tudun Jukun Zariya
a Jihar Kaduna. Da yake yanke hukunci bayan kwashe watanni
ana shari’ar da aka gabatar da kwararan shaidu
biyar, alkalin Mai shari’a Mannir Ladan ya ce duk da
tsawon lokacin da aka kwashe ana sauraron
shari’ar wanda ake zargin ya kasa kare kansa. Don
haka a karkashin tsarin mulki da kundin dokoki na Final Kod na Jihar Kaduna, sashi na 258 (1) kotun
ta yake masa hukuncin daurin rai-da-rai. Bayan yake hukuncin lauyar gwamnati mai gabatar
da kara, Hajya Safiya T. Zailani ta yi wa Aminiya
karin bayani a kan shari’ar inda ta ce, “An fara
sauraren karar ce ranar 14 ga Disamban bara kuma
an yanke hukunci a ranar 16 ga Mayun bana bayan
mun gabatar da shaidu biyar, yara biyu daga cikin wadanda ya lalata da likitan da ya duba lafiyar
yaran da dan sanda mai bicike da wakilin al’ummar
unguwa, wadanda suka tabbatar da ya aikata
laifin.” Idan za a tuna a Aminiya ta ranar 6 ga Oktoban
bara mun kawo labarin kama Husaini dan Daura,
wanda a lokacin ya ce idan yaran za su wuce
makaranta sukan biyo ta dakin da yake gudanar
da sana’ar tsibbu don sha ruwa, shi kuma sai ya yi
amfani da wannan damar ya yi lalata da su. Ya ce ya dauki dogon lokaci yana wannan ta’asa da
yaran kafin dubunsa ta cika. A wani labarin Mai shari’a Mannir Ladan na Babbar
Kotu ta daya da ke Zariya, ya yanke wa wani
magidanci mai suna Sunday Anner mai shekara 63
daurin shekara 20 a gidan yari tare da biyan Naira
dubu 20 bayan samunsa da laifin yi wa wata
dalibar coci fyade. Lauyan gwamnati da ta tsaya wa dalibar Hajiya
Jumai Adamu dan’Azumi ta ce, shekara hudu da
suka wuce ne aka gabatar da Sunday Anner ana
tuhumarsa da yi wa wata dalibar coci ’yar shekara
13 fyade, kuma bayan gamsar da mai shari’a da
kwararan shaidu guda shida kuma wanda ake tuhumar ya kasa kare kansa, sai alkalin ya yanke
masa hukunci daurin shekara 20 da biyan Naira
dubu 20 a karkashin sashi na 283 na Final Kod.
.
Source @aminiya
COMMENTS