Blog Archive

Powered by Blogger.

Ina Tsoron Karfin ’Yan Adawa, inji Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk da karfin mulkin da yake da shi yana tsoron kare gwamnatinsa musammam a gurin ‘yan adawa....


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa duk da karfin mulkin da yake da shi yana tsoron kare gwamnatinsa musammam a gurin ‘yan adawa. Buhari ya ce gwamnatinsa na fama da makarkashiya ta kowane bangare daga ‘yan adawa, wadanda kuma hana su kulla irin wannan makarkashiya abu ne mai wahalar gaske. Ya fadi hakan ne a fadarsa da ke Aso Rock Billa a Abuja jiya Juma’a lokacin da yake karbar bakuncin kungiyar yada manufar Buhari ta kafar sadarwar zamani wato Buhari Media Organisation. Haka kuma shugabn kasar ya ci gaba da cewa, abu ne mai wahalar gaske masoyansa su iya kare gwamnatinsa musamman a wurin ‘yan adawa.. Ya jinjinawa kokarin mambobin kungiyar na bayyana manufar gwamnatin ta sa duk da matsananciyar wahalar da suke sha musamman a wajen ‘yan adawa. “Na san kuna yin matukar kokari wajen gudanar da ayyukanku, kasancewar abin da kuka sa a gaba abu ne mai wahala. Domin ba abu ne mai sauki ba, a yi kokarin fahimtar da jama’a kan inda wannan gwamnati ta sa gaba musamman ma lokacin da kuke kokarin kare ni. “Na san wannan gagarumin aiki da kuke yi babu wanda ya isa ya biya ku, aiki ne na sadaukarwa, sakamakonsa na gurin Allah. Domin aiki ne da kuke yi da karfinku da kudinku da kuma tunaninku. “Duk da cewa, ‘yan adawa na ci gaba da yi wa wannan gwamnati zagon kasa, ba zai sa mu fasa abin da muke yi ba,” . Shugaban kasa Muhammadu Buhai, tare da sakataren gwamnatin tarayya Mista, Boss Mustapher (na 6 daga dama) da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Malam Abba Kyari lokacin da mambobin kungiyar Buhari Media Organisation karkashin jagorancin Mista Austin Buraimoh ( na 5 daga dama) a state House da ke Abuja.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Ina Tsoron Karfin ’Yan Adawa, inji Shugaba Buhari
Ina Tsoron Karfin ’Yan Adawa, inji Shugaba Buhari
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgnV81iP9PInBdV6FGhAoTrO9Qx3DvJZkyEMiqyEcB4dXCXVWIa7UmChSgGnkzQIZ04_UOMHT1OYZ_GiGi1Vdxj8hlY5isRX2WxuM39IRTsDdLFE_9Z66Yvw-_8mtB1H8XNW0Ut5L7HsHQi/s320/BUHARI.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgnV81iP9PInBdV6FGhAoTrO9Qx3DvJZkyEMiqyEcB4dXCXVWIa7UmChSgGnkzQIZ04_UOMHT1OYZ_GiGi1Vdxj8hlY5isRX2WxuM39IRTsDdLFE_9Z66Yvw-_8mtB1H8XNW0Ut5L7HsHQi/s72-c/BUHARI.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/ina-tsoron-karfin-yan-adawa-inji.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/ina-tsoron-karfin-yan-adawa-inji.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy