Wani Malamin Addinin Musulunci mai ra’ayin rikau da ke Kaduna, Shaikh Ahmad Gumi, ya yi wa Shugaba Buhari shagube tare da zargin barin jahil...

Wani Malamin Addinin Musulunci mai ra’ayin rikau
da ke Kaduna, Shaikh Ahmad Gumi, ya yi wa
Shugaba Buhari shagube tare da zargin barin
jahilan mashawarta da kuma mutanan da sam ba
su da tausayin al’umma a zagaye da shi. Wannan zargin da Malamin na Musulunci ya yi, ya
biyo bayan nu na hoton tsohon gwamnan Jihar
Kaduna ne, Ramalan Mukhtar Yero, rike da allon
tuhumar da ake yi masa. Da yake yin bayanan bayan kammala karatun
tafsirin da yake yi a Masallacin Sultan Bello, da ke
Kaduna, ranar Alhamis, Shaikh Gumi, ya kwatanta
mashawartan Shugaba Buharin ne da
mahaukata, domin a cewarsa, “sam ba sa tare da
mutane.” “Sun kulle Shugaban kasa, ba wanda zai iya gaya
masa gaskiya. “Gaya mani mai hankalin da ke a tare da shi
cikinsu. Ba wanda zai iya gaya masa gaskiya. Malamin na Musulunci ya ce, babbar hanyar
samun nasara ita ce, yafiya, gaskiya, da kuma
kiran mutane da su aikata alheri da kuma gudan
shawarar jahilai. “Amma tafarkin da wannan gwamnatin ke tafiya
a kansa ya nu na a fili cewa tana bin shawarar
jahilai ne. “Idan mun kyale shi ya kai kasan nan ga halaka,
ba shi kadai ne zai halaka ba, dukkan mu ne. “A kullum mu na gaya wa Buhari gaskiya, amma
ba ya sauraro domin sun kulle shi. “Annabin Allah Ya na yafiya, amma Buhari ba ya
yi. “Annabin Allah ba ya tarayya da jahilai, amma
Buhari kullum yana son su, yana kuma tare da
jahilan,” in ji shi. “Kokari muke mu sanya Buhari a kan hanya ta
gaskiya,” in ji Shaikh Gumi.
.
Copyright @leadershipayau
COMMENTS