An bukaci gwamnatocin jihohin Arewacin kasar nan da su ribanya kokarin da suke yi bisa yaki da hana yawaitar fatauci da shan miyagun kwayoyi...
An bukaci gwamnatocin jihohin Arewacin kasar nan da su ribanya kokarin da suke yi bisa yaki da hana yawaitar fatauci da shan miyagun kwayoyi a sakanin matasa don magance karuwar gurbacewar dabi’u, a tsakanin matasan kasar nan. Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Izalatil Bid ah Wa”Ikamatis Sunnah [JIBWIS], na kasa Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ne ya’yi wannan kira ya yin da yake gudanar da Tafsiri wa dimbin mata a garin Tilden Fulani a ci gaba da ziyarar gudanar da tafsiri da yake yi wa mata, ya ce shan kwayoyi masu sa maye ya saba wa karantarwar addinin Musulunci kuma yana nakasa al’umma da ci gaban tattalin arzikin kasa. Sheikh Jingir wanda ya yi Allah wadai da yawaitar samun rahotannin kasha-kashen mutane ba gaira ba da lili da ake samu yanzu a kasar nan, ya hori matan da a koyauce su zama suna ma yayansu addu’o in fatan alkhairi kuma su zama masu kula da tarbiyarsu don su zama ya’ya nagari masu hazakar neman halaliyarsu. Ya kara yin kira ga gwamnonin jihohin Arewacin kasar da su wadata manomansu da takin zamani domin su sami nome isassen abinci a wannan daminar. Shiekh Jingir, ya yaba wa kokarin da gwamnati mai ci yanzu karkashin shugabancin Muhammadu Buhari, ke yi na inganta aikin gona ya ce hakan zai kara karfafa tattalin arzikin kasar ya sa ta zama mai dogaro da kanta wajen shiyar da al’ummarta. Ya yi Allah wadai da masu jefa kalaman batanci wa wannan gwamnati musamman mutanen Arewacin kasar nan ya ce rashin la’akari ne da abubuwan da suka yi ta faruwa alokacin da gwamnatin da ta gabata karkashin shugabanci Dakta Good-Luck Jonathan, yasa wadansu daga cikin mutanen Arewacin kasar sukeyin suka wa gwamnatin da take mulki a yanzu. Shiekh Jingir ya’yi amfani da wannan daman wajen yin kira ga yan Nijeriya da su tabbata sun je sun yi rijistar katin dan kasa don su sami tsira da ‘yancinsu a duk inda suka sami kansu a cikin fadin tarayyar kasar nan. Tun a fari a fassarar tafsirinsa a cikin Suratul Al-hakka, Shiekh Jingir, ya hori al’ummar Musulmi da koyaushe su zama suna gudanar da ayyukansu na yau da kullum bisa karantarwar Alkur’ani. Ya ce domin Alkur’ani, sako ne daga Allahu Subahanahu Wa Ta’ala, da ya saukar wa ma aiki S. A.W. ta Mala’ika Jibirilu, don ya isar wa dukkan halitta da ke bisa doron duniya.Copyright @leadershipayau
COMMENTS