Blog Archive

Powered by Blogger.

A Zaben 2019: Ku zabi wanda kuka gadama Inji shugaba– Buhar

A daidai lokacin da ake kara kusantar babban zabe na 2019, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar kasar nan da su tabbatar s...


A daidai lokacin da ake kara kusantar babban zabe na 2019, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi kira ga al’ummar kasar nan da su tabbatar sun yi katin zabe, sannan kuma ya ce su zabi duk wanda suka ga dama a lokacin zabukan. Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a ranar Talatar
da ta gabata, a lokacin da yake karbar bakuncin jami’an bangaren Shari’a karkashin jagorancin Alkali a Kotun koli na kasa, Mai Shari’a Okukayode Ariwoola don shan ruwa bayan kammala Azumin Ramadan na ranar a fadarsa. Buhari wanda ya ce harkokin kimiyya ne suka taimaka wajen tabbatuwar nasarar da ya samu a zaben 2015, a lokacin da yake maida jawabi bayan da tsohon Babban Jojin Najeriya, Mai Shari’a Alfa Balgore ya kare jawabi. Shugaban kasar ya kara da cewa a sau da dama ya yi ta zaburar da gwamnoni da su kara maida hankali wajen jan hankalin jama’arsu kan muhimmancin yin katin zabe ta yadda za su maida shi ya zama shaidar zama ‘yan kasa. “Na yanke shawarar gayyatarku ne saboda ba kowane lokaci nake ganinku ba. Ina sake jaddada abin da na fada ne bayan da na ji abin da ku ka fada. Na taba ambatar haka a lokacin da nake aikin soja sannan kuma ga kuruciya muna matasa, a lokacin mun yi imanin cewa al’amura suna tafiya a baibai. Don haka a lokacin da na zama shugaban kasa na mulkin soja sai na kame dukkan shugabanni har shugaban kasa na kulle su a kirikiri, na ce ku ma su laifi ne har sai kun bayyana kanku a matsayin marasa laifin. Sannan muka kafa kotunan wucin gadi don yin bincike da kuma hukunci, kuma har yanzu ina tuna irin nagartattun mutanen da Allah Ya albarkaci Najeriya da su, amma karancinsu ya sanya ba a ganin gudumawar da suka bayar a cikin al’umma.” Ya ci gaba da cewa, “daga baya na yanke shawarar sake neman shugabancin kasar nan a farin kaya, inda ya tsaya takara har sau uku, a na hudun ne Allah Ya ba ni nasara. Don haka nake kara godiya ga Allah da kuma tsarin kimiyyar tantance kuri’u, saboda katin zabe na dindindin da kuma na’urar tantance kuri’a na da muhimmanci. Don haka duk wanda ya yanki katin ya kuma jefa kuri’arsa, to hakika za a kirga ta.” Ya kara da cewa, “gabanin haka ana jirkita kuri’u sannan kuma ana rubuta sakamakon zabe, kuma babu yadda zaka yi a gaban alkali wajen kare magudin da aka yi maka don samun nasara, amma a yau da tauimakon kimiyya lamuran sun saukaka ainun. Da wannan ne na yi ta zaburar da gwamnoni
da su kara maida hankali wajen jan hankalin jama’arsu kan muhimmancin yin katin zabe ta yadda za su maida shi ya zama shaidar zama ‘yan kasa. Don haka ‘yan Najeriya su zabi duk wanda suke so a dukkan kabilu da addinai, sannan su nuna wa shugabanin nasa hakan. Daga nan sai Mai Shari’a Alfa Balgore ya tabbatar da cewa Buhari masoyin Najeriya ne matuka, ya ce amma shugaban na bukatar mutanen kirki ne a kusa da shi kowane lokaci.
.
Source @aminiya

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: A Zaben 2019: Ku zabi wanda kuka gadama Inji shugaba– Buhar
A Zaben 2019: Ku zabi wanda kuka gadama Inji shugaba– Buhar
http://fm.nextwapblog.com/files/6475/buhari.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/a-zaben-2019-ku-zabi-wanda-kuka-gadama.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/a-zaben-2019-ku-zabi-wanda-kuka-gadama.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy