Ranar Alhamis da ta wuce ne, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsallake rijiya da baya, yayin da jirgi mai saukar ungulu da...

Ranar Alhamis da ta wuce ne, mataimakin
shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tsallake rijiya da baya, yayin da jirgi
mai saukar ungulu da yake ciki ya fara fitar da
hayaki.Hakan ya sanya aka tilastawa jirgin sauka
a garin Abuja kuma jirgin ya kai Yemi Osibanjo ne
taro a kwalejin hukumar kwastam da ke
Gwagwalada a cikin garin Abuja. Osinbajo ya je kwalejin ne don halartar taron
yaye manyan jami’an hukumar na wannan
shekarar kuma dama jirgin ne ya kai Mataimakin
wurin taron. An ruwaito cewar, jirgin bai riga ya yi nisa da
kasa ba, inda aka tilasata wa jirgin sauka bayan
da ya fara fitar da hayaki, inda hakan ya sanya
aka dauke mataimakin daga wurin ya tafi ta
hanya
.
Copyright @leadershipayau
COMMENTS