Blog Archive

Powered by Blogger.

Tausayin Buhari nake – Inji Ahmad Gumi

Irin yadda Dokta Ahmad Abubakar Gumi yake yawan yin maganganun da suke haifar da cece-ku- ce yana sa mutane nuna rashin jin dadinsu a kai. A...


Irin yadda Dokta Ahmad Abubakar Gumi yake
yawan yin maganganun da suke haifar da cece-ku-
ce yana sa mutane nuna rashin jin dadinsu a kai. A
makon jiya ne Dokta Gumi ya fito ya kira ’yan
Arewa magoya bayan Shugaba Buhari da dakikai
lamarin da ya jawo cece-ku-ce a kafofin watsa labarai da na sadarwar zamani. Dokta Gumi kan yi
magana a kan kusan komai, ta yadda a wasu
lokuta wadansu suke ganin ba ya tauna magana
kafin ya furzar da ita. Irin wadannan kalamai na
Dokta Ahmad Gumi ba wai sun tsaya a kan
harkokin addini ba ne inda yake da masaniya, har ma sukan shafi harkokin siyasa da shugabanci. Sai
dai hatta a bangaren addini kamar sauran
bangarorin da yake tabowa akan zarge shi da
naciya da kafiya kan dole sai an bi abin da ya
fahimta. Wannan ya sa hatta malaman addinin
Musulunci na da da na yanzu ba su tsira daga suka daga gare shi ba, kamar yadda marigayi Sheikh
Muhammad Awwal Albani Zariya ya faba fadi a
kansa. Koda da wakilinmu ya tuntubi Dokta Gumi
kan maganarsa ta baya-bayan nan da da ya kira
’yan Arewa magoya bayan Shugaban kasa
Muhammadu Buhari da dakikai, sai ya ce ai ba shi ne ya fara kiransu da haka ba, kuma ba yana nufin
dukansu ba ne. Sannan mun dauko bayanin da
marigayin Sheikh Albani Zariya ya taba yi kan
malamin wanda ke yawo a shafin Youtube, inda
bayan ya yabi marigayi Sheikh Abubakar Gumi ya
kuma caccaki salon Dokta Ahmad Gumin: An ce ka ambaci ’yan Arewa masu goyon bayan
Buhari da dakikai, haka ne? (Dariya) Ai ba ni na fara cewa da su dakikai ba. Shi
ma Shugaban kasa ai ya ce da su cima-zaune ko,
wadansu kuma jahilai. Baya ga haka kuma ai duk
wata magana ba za a ce an taru an zama daya ba
ko. Ma’ana ko mutum ya ce dukan mutane barayi ne ai
ka ga babu yadda za a ce kowa barawo ne domin
dole akwai mutanen kirki ko. Wadansu na ganin saboda ba ka goyon bayan
Shugaban kasa shi ya sa kake zafi a kansa
yayin tafsirinka, me za ka ce? A’a abin da ya sa nake zafi shi ne mutane suna
kokawa kan halin da suke ciki a kasar nan. Yanzu
haka wadansu sun aiko min da tes cewa akwai
yunwa a kasa. Ga rashin tsaro da kuma cutar
mutane. Ko kai idan wani abu ya same ka ba zan ji
dadi ba. Talakawa na cikin wani hali. Yanzu haka jiya (ranar Talata) kusan kauyuka bakwai ’yan
ta’addan Zamfara suka tayar. Mutane da yawa a yanzu haka suna korafin ba su
iya cin abinci. Muna cikin wani hali a kasar nan, don
haka ta yaya zan yi shiru? Ba zai taba yiwuwa ba.
Kuma idan ka yi kokarin fada wa wadanda ke da
alhakin gyara sai wadansu su ga kamar ba ka
kyauta ba. Ni kuma ba dan siyasa ba ne, kokari kawai nake na ganin an samu sauki a kasa. Idan
kuwa za ka gaya wa mutum gaskiya dole ka nuna
masa cewa shi fa mutum ne kamar kowa da bai fi
karfin kuskure ba. Shi ma wanda ake ganin yana kuskure sai a fada
masa domin duk a zo a hada hannu domin gyara
kura-kurenmu. Dukanmu ’yan Adam ne da ke
kura-kurai babu wanda ya fi karfin yin kuskure. Idan an ce na yi zafi yanzu na fara? A lokacin
PDP me ya sa ba a ce na yi zafi ba? Lokacin
Jonathan me ya sa ba a ce na yi zafi ba sai
yanzu? An ce wai ba ka goyi bayan Buhari ba ko a
zaben 2015? Ban goyi bayansa ba ne saboda na san akwai
wadanda suke son yin amfani da shi. Shi ya sa na
ce ya bari a kawo wani matashi mai jini a jiki daga
Arewa a buga da shi. Wannan kasa tana cikin
matsala saboda haka abu ne mai wahala gare shi
ya magance matsalolin kasar nan. Ni tausayinsa nake yi amma ba wai na ki shi ne ba. Shin kana damuwa da irin kalaman da ake yi a
kanka saboda maganganunka? Ni duk haushin da ake yi bai damuna ko kadan.
Haushin kare bai damuna, idan dai kai ba barawo
ba ne don ka ji kare na haushi ai bai kamata ya
dame ka ba. Ko Malam ya gamsu da yaki da rashawa da
gwamnatin nan ke yi? Ai da wuya a samu gaskiya a cikin batun yaki da
cin hanci da rashawa, rashin gaskiyar ba daga
Shugaban kasar ba ne a’a daga mutanen da zai yi
amfani da su ne wajen aikin. Misali kana da aiki mai
kyau da kake son yi amma kuma ba ka da
injiniyoyin kwarai da za su taimaka maka ta yaya za a yi aiki ya yi kyau. Ni dama tun farko na san ba ya da mutanen kirki
da za su taimaka masa. Farfaganda ce kawai da
ake yi da batun domin cimma wani buri na siyasa
nake adawa da shi kawai. Wace shawara za ka bai wa wannan gwamnati
domin ta gyara kura-kuran da take yi? Shawarata kawai gare shi da jam’iyyarsa shi ne ya
yi koyi da matakin marigayi Mandela cikin mutunci.
Ita kuwa jam’iyyar ta fito da mutumin kirki ba tare
da cin rashawa ba. Su fitar ko tsayar da mutumin da zai samu karbuwa
wajen mutane dan Arewa. Sannan dukansu ’yan takarar su zo su fada mana
abubuwan da za su yi wa mutane da kasa daga
nan sai a tantance wanda ake so domin a zauna
lafiya.
.
Copyright @aminiya

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Tausayin Buhari nake – Inji Ahmad Gumi
Tausayin Buhari nake – Inji Ahmad Gumi
https://etiketa.com.ng/wp-content/uploads/2018/06/gumi-buhari-720x340-678x340.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/tausayin-buhari-nake-inji-ahmad-gumi.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/tausayin-buhari-nake-inji-ahmad-gumi.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy