Wani dan majalisar wakilan Najeriya ya bayyana cewa babu abun da ake fama da shi a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari da ya wuce yunwa da bakar...
Wani dan majalisar wakilan Najeriya ya bayyana cewa babu abun da ake fama da shi a
mulkin Shugaba Muhammadu Buhari da ya
wuce yunwa da bakar wahala. Kalaman Jagaba Adams Jagaba, wanda ke
wakilatar Kachia da Kagarko daga jihar Kaduna, na
zuwa ne bayan da majalisun kasa suka ka yi
barazanar daukar mataki kan shugaban idan bai
aiwatar da kudurorin da suka zartar ba. A ranar Talata ne majalisun dokokin kasar suka
amince da wasu kudurori 12 da suka ce wajibi ne
gwamnatin Muhamadu Buhari ta aiwatar da su ko
kuma su dauki mataki. Sai dai har yanzu babu wani martani da fadar
shugaban kasar ta mayar. Amma rahotanni sun ambato wani dan majalisa mai
goyon bayan shugaban, Muhammed Gudaji
Kazaure, na cewa an dora wa wasu takwarorinsa
alhakin fara yunkurin tsige shugaban, amma ba za
su "bari ya yi tasiri ba". Mista Jagaba ya ce idan har Shugaba Buhari bai
aiwatar da kudurorin da suka bukata ba to za su
tsige shi a bisa tsarin kundin mulkin kasa. Ya kara da cewa ba sa shakkar yiwuwar hakan
don "Buharin ba Allah ba ne kuma bai yi kama da
Annabi ba, duk inda ya yi kuskure za mu take shi"
in ji dan majalisar. Ku latsa hoton da ke kasa don sauraron hirar
Adams Jagaba da Yusuf Tijjani na BBC: Zaman da majalisun dokokin suka yi dai na zuwa
ne a lokacin da rashin jituwa ke kara fitowa fili
tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma
shugabannin majalisar. Jerin kudurorin da suka cimma a zaman: Kawo karshen kashe-kashe a Najeriya A daina tsangwama da kuma muzguna wa
wadansu 'yan majalisa Gwamnati ta rika bin doka da oda Shugaban kasa ya dauki mataki kan wadansu
wadanda ya nada mukamai Ya yi yaki da cin hanci da rashawa tsakaninsa
da Allah Ya daina sanya baki kan al'amurran da suka
shafi majalisar Majalisar dokokin kasar za ta fara tuntubar
Majalisar Dinkin Duniya don ceto
demokradiyyar Najeriya Majalisar za ta tuntubi kungiyoyi masu rajin
kare demokradiyya don ceto demokradiyyar
kasar Shugaban kasa ya magance matsalar rashin
aikin yi da kuma talauci a kasar Duka majalisoshin biyu sun nuna goyon baya
ga shugabancin Bukola Saraki da kuma
Yakubu Dogara Kuma ba sa goyon shugabancin Sufeto Janar
na 'yan sanda Najeriya Ibrahim Idris Majalisa za ta dauki mataki kamar yadda tsarin
mulki ya ba ta dama, idan aka ki yin wani abu. Wadansu na ganin barazanar daukar matakin da
tsarin mulki ya ba su kamar yadda suka yi ikirari zai
iya hada wa da yunkurin tsige Shugaba Buhari A ranar Litinin 'yan sandan kasar suka gayyaci
Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Bukola Saraki
domin amsa tambayoyi kan zargin daukar nauyin
'yan fashi da makami a mahaifarsa ta jihar Kwara. Sai dai daga bisani Sanata Saraki ya ce sun shaida
masa cewa sun janye gayyatar, kawai suna bukatar
"ya amsa ne a rubuce". Rahotanni sun kuma ce an rage yawan jami'an
tsaron farin kaya da ke bin tawagar Saraki da kuma
Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, da kuma
mataimakansu. Wannan batu ne kuma ya sa kungiyar tsoffin 'yan
sabuwar PDP, wacce Saraki da Kakakin Majalisar
Wakilai Yakubu Dogara ke kan gaba a ciki, suka ce
sun dakatar da tattaunawar da suke yi da
gwamnatin kasar da kuma jam'iyyar APC. Suna dai zargin cewa an mayar da su saniyar-ware
ne tare da yi musu bi-ta-da-kulli, a gwamnatin da
suka taimaka aka kafa. A baya dai gwamnatin ta sha musanta wannan
zargi.
.
Copyright @bbchausa
COMMENTS