Abubuwan fashewa sun kashe a kalla mutum 17 tare da jikkata wasu mutanen 80, tare da lalata wani masallaci a babban birnin kasar Iraki, in j...

Abubuwan fashewa sun kashe a kalla mutum
17 tare da jikkata wasu mutanen 80, tare da
lalata wani masallaci a babban birnin kasar
Iraki, in ji majiyoyin lafiya. Gwamnatin kasar ta ce fashe-fashen na daren
Laraba sun faru ne sanadiyyar fashewar ma'ajiyar
makamai a unguwar 'yan Shia da ke birnin Sadr. Sai dai ta bayar da bayanin ainihin inda ma'ajiyar
makaman take ba, amma wasu jami'an tsaro sun ce
a cikin masallacin ne. Magoyan bayan malamin Shi'ia Moqtada Sadr su ne
suke amfani da masallacin. Mista Sadr ya jagoranci wani kawance na kishin
kasa wanda ya hada da wasu kungiyoyin da ba na
addini ba a zaben 'yan majalisar dokokin da aka yi
a watan jiya, inda ya ci 54 daga cikin kujeru 328. Ya kuma jagoranci mayakan da suka yaki dakarun
Amurka bayan sun far wa Iraki a shekarar 2003,
amma a shekarun baya-bayan nan yana taimaka
wa sojojin Irakin da Amurka ke mara wa baya a
yakin da suke yi da 'yan IS masu ikirarin jihadi. Wata majiyar 'yan sanda ta shaida wa kamfanin
dillancin labaran AFP cewar tarin makaman na wata
kungiyar 'yan bindiga ce, kuma makaman sun
hada da gurneti da rokoki. Gwamnatin ta ce ana kan bincike domin gano abin
da ya sa ma'ajiyar makaman ya fashe, amma wani
rahoto ya ce an yi imanin cewar ya faru ne a lokacin
da ake son a kai makamai wata motar da aka ajiye
kusa da wurin. Hotunan da aka dauka bayan fashe-fashen sun
nuna cewa fashewar makaman ta daidaita
masallacin tare da lalata gidajen da suke kusa da
kuma wasu gine-ginen.
.
Copyrigh @bbchausa
COMMENTS