Blog Archive

Powered by Blogger.

Buhari na tattara shaidun boge domin ya daure ni. Inji - Obasanjo

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari na tattara shaidun boge domin ya daure shi saboda suka...


Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo
ya yi zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari
na tattara shaidun boge domin ya daure shi
saboda sukar da yake masa. "Wadansu majiyoyi na tsaro sun tabbatar min da
cewa gwamnati na shirin amfani da hukumar EFCC
da wasu shaidun boge domin kama ni da kuma
tsare ni na din-din-din," a cewarsa. Wannan zargi na kunshe ne a wata sanarwa da mai
magana da yawun Mr Obasanjo, Kehinde Akinyemi,
ya fitar a birnin Abeokuta ranar Juma'a, wadda
kafafen yada labaran kasar suka wallafa. Takun saka ya zafafa tsakanin shugabannin biyu
tun bayan da Mr Obasanjo, wanda ya goyi bayan
Buhari a zaben 2015, ya yi Allah-wadai da yadda
yake gudanar da mulki, sannan ya ce bai cancanci
a sake zabarsa ba a zaben 2019. A 'yan kwanaki ne shi kuma Buhari ya zargi
gwamnatin Obasanjo, wanda ya mulki kasar a
matsayin zababben shugaba daga 1999 zuwa
2007, da "kashe dubban daloli kan wutar lantarki
ba tare da an ga wutar a kasa ba". Obasanjo ya
musanta wannan zargi. Kawo yanzu babu wani martani daga fadar
shugaban kasa, kuma BBC ba ta yi nasarar jin ta
bakinsu ba kawo yanzu. Abin da sanarwar ta kunsa Sanarwar ta ce wasu majiyoyin tsaro sun yi zargin
cewa Mr Obasanjo na cikin jerin sunayen mutanen
da suke farauta, kuma rayuwarsa na cikin hadari. "A cewar majiyoyin, yawancin jami'an tsaron suna
kusa da gwamnati, kuma a kullum suna kokarin
bin hanyoyin da za su iya kawar da 'yancin da
tsohon shugaban yake da shi domin kama shi da
laifi." Sanarwar ta kara da cewa: "Haka kawai ba za mu
ba wadannan rahotannin muhimmaci ba, amma
saboda yawancin wadanda suka kwarmata
bayanan ba su saba bayar da bayanan karya ba." "Wannan gwamnati tana nuna ba ta damu ba, wani
lokaci tana dogaro da ayyukanta, a kullum ana
rasa rayuka da dukiyoyi a jihohi da dama na kasar
nan" "Yanzu muna cikin kasar da mutum mai daraja ta
uku da na hudu ke fuskantar barazana daga
gwamnatin da suke yi wa aiki." "Akwai wasu a kasar nan yanzu da ke cikin
fargaba saboda ana iya farautarsu a ci mutuncinsu
ko ma a kashe su kamar yadda yakin 2019 ya
dauki wannan salon" Sanarwar ta kuma ce "bayanan sun nuna abubuwa
guda biyu a yanzu, na farko shi ne ana iya kwace
Fasfo dinsa a daure shi har abada, domin hana shi
sake yin tsokaci game da lamurran da suka shafi
gwamnati da tafiyar da tattalin arziki da kuma
tsaron 'yan kasa da dukiyoyinsu. "Abu na biyu kuma shi ne, gwamnati na son amfani
da hukumar EFCC domin sake bude bincike kan
ayyukan gwamnatin tsohon shugaban ta hanyar
amfani da bayanai da shedu na karya." Sabanin Obasanjo da Buhari Obasanjo ya goyi bayan Buhari a zaben 2015 A watan Janairun 2018 ne Obasanjo ya bukaci
Buhari kada ya nemi wa'adin shugabanci na
biyu Obasanjo ya ce Buhari ya gaza inda ya bukaci
ya sauka cikin mutunci bayan wa'adinsa na
farko A martaninta, gwamnatin Buhari ta ce ba za ta
iya muhawara da Obasanjo ba Ministan watsa labaria Lai Mohammed ya ce
idon Obasanjo ya rufe ga nasarorin gwamnatin
Buhari Buhari da Obasanjo sun hadu a taron Tarayyar
Afirka a birnin Addis Ababa na Habasha a ranar
28 ga Janairu A watan Afrilu Obasanjo ya jaddada cewa
Buhari ya gaza wajen ciyar da Najeriya gaba. Obasanjo ya ce bai kamata a sake zaben Buhari
ba saboda gazawarsa. Obasanjo ya kafa wata kungiyar siyasa bayan
ya caccaki gwamnatin Buhari A ranar 22 ga Mayu Buhari ya soki gwamnatin
Obasanjo kan lantarki Buhari ya ce wani tsohon shugaban kasa ya
kashe dala biliyan 16, kuma har yanzu ba
lantarki Obasanjo ya mayar wa Buhari da martani a
ranar 22 ga Mayu Obasanjo ya ce gwamnatin Marigayi Umaru
'Yar'adu ta kafa kwamitin bincike, kuma
kwamitin ya wanke shi
.
Copyright @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Buhari na tattara shaidun boge domin ya daure ni. Inji - Obasanjo
Buhari na tattara shaidun boge domin ya daure ni. Inji - Obasanjo
https://hausa.premiumtimesng.com/wp-content/files/sites/4/2018/01/Obasanjo-Buhari.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/buhari-na-tattara-shaidun-boge-domin-ya.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/06/buhari-na-tattara-shaidun-boge-domin-ya.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy