Lokacin da Musa wani dan makarantar gaba da sakandare (babbar makaranta) ya fara tari da kuma ciwon kirji, na wasu makonni, shi bai danganta...
Lokacin da Musa wani dan makarantar gaba da sakandare (babbar makaranta) ya fara tari da kuma ciwon kirji, na wasu makonni, shi bai danganta hakan ba, da ‘shisha’ ko kuma wadda aka sani da hooka, ko kuma wata kafa da ake amfani da ita, ana jin dadi ga su masu yin ita harkar. Shi da abokan sa suna haduwa a wani wuri ku san kullun saboda su rika sheke ayarsu. Duk sai ya rika yin watsi da duk wata shawarar kirki da za a bashi, saboda shi a na shi ganin yana sha ne, saboda kawai yana shakar wani abu ne wanda ya sha bam ban, da irin na tabar asali, saboda ai tamkar ana dama tane da ruwa, ba wai sigari ba. Amma duk da wasu boye boyen da yake yi sai ga shi bayan an gwada shi, an gano cewar ya kamu da cutar tarin fuka, ‘yan makonni bayana n samu abokan harkar shi, suma sun kamu da cutar tarin fuka. Shi hookah wani abu ne na zamani wanda kuma ake amfani da shi lokacin da ake shan,wata taba mai wani armashi,da masu amfani da ita suke so, (shisha), ko kuma wani lokaci cannabis,wanda hayakin na shi ne, a ke shan ta, wanda kuma yake wucewa ta wani abu wanda ya kunshi ruwa, sau da yawa gila shi, kafin a kai ga shaka. Ga wasu su al’amarin shan shisha wata dama ce da suke samu domin su, samu shakatawa, bama kamar idan sun yi wasu ayyukan da suka gajiyar dasu, wannan su wani jin dadi ne , bama kamar idan suna tare da abokansu. Yawancin matasa suna karuwa a maganar shan hookah, yanzu kuma akwai irin hakan a wasu gidaje a Nijeriya, saboda ajiye da ita. Wasu mutane suna ganin shan shisha ba wani abu bane mai cutarwa, don haka abin bai damuwar lafiya, wato kamar sigari da sauran wasu nau’i nau’i na abubuwan da suka danganci taba, akwai wadanda suna ma kara taba wiwi kafin su sha ta. Su kuma masana bangaren da ya shafi lafiya sun ja kunnen al’umma cewar shan shisha yana cutarwa, ga lafiya. Shan shisha wani al’amari ne wanda yanzu a Nijeriya yake samun ci gaba, yana kuma samun karbuwa, musamman atsakanin matasa, kamar dai yadda Dokta Nnenna Ezeigwe, wadda take wata shugaba ce ta Non Communicable Diseases ta ma’aikatar lafiya ta taryya ta bayyana. Ta kara bayyana cewar ‘’ Al’amarin shisha abin yana samun karbuwa a birane, abin kuma yana wata tafiya kamar wutar daji, abin ban takaici ne, yadda ita shisha ta kasance tana nan koda yaushe masu son amfani da ita suka bukata, ba wata wahala gare ta ba, har ma ta hanyar fasahar zamani ta yanar gizo, kop kuma intrenet. Abu daya kuma mai ban haushi shi ne ko su wadanda suka yi shisha basu san abubuwan data kunsha ba, wasu ma suna gani wani nau’i na taba ne wanda baya cutarwa’’. Dokta Ezeige ta jaddada cewar ba kamar yadda wasu suka sani bane, maganar gaskiya ita ce shisha ta fi taba sigari cutarwa. Wannan abin ya kasance haka ne saboda shi al’amari shan shisha ya kan dauki awa daya, bugu da kari kuma bincike ya nuna a daidai lokacin da ake shan ita shishar, abu mai yiyuwa ne asha kamar karan taba sigari guda dari (100). ‘’Akwai kuma mutane da yawa wadanda suke ganin shan shisha ba wani abinda zai kasance ya zame wa mutum jiki ba, wanda har zai ji idan bai yi ba, to ba wata maganar wani jin dadi a tare da shi. Saboda ruwan da ake amfani da shi, ta shi, wannan makurarin, shi kan shi zai tsoshe nicotine, wannan kum aba wani abu bane ga mashaya shisha, amma kuma duk da hakan suna cikin tsaka mai wuya saboda kuwa da akwai nicotine mai yawa wadda za ta iya samar da matsala, yana kuma da kwai a gane cewar ko shi hayakin shisha yana da cutarwa ga wasu mutane bama kawai ga su masu shan ta ba kadai donn haka sai ta ja kunne mutane’’ Ta ce, shisha tab ace ta kuma kunshi nicotine, wanda shi ne mai cutarwa da kuma , irin shine ita taba ta asali ta kunsa, har ma da sauran abubuwan da suke cutarwa, yawancinsu kuma ana kiransu carcinogens. Bayan kansa ta kara cewar shisha kamar duk wata sigari wani nau’i ne na wasu cututtukan da basu da saurin yaduwa, kamar su cardiobascular, cutar ciwon sikari, da kuma matsalar samun isasshen numfashi, da abin ya hada da asthma. Hakanan ma an danganta ita cutar periodontal da ita shisha, sa
COMMENTS