Blog Archive

Powered by Blogger.

Shugaba Buhari Ya Bukaci Coci Su Rinka Wa’azi akan hadin Kan Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga malaman addinin kirista dake kasar nan dasu dinga yin amfani da matsayinsu wajen dabbaka zaman ...


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga malaman addinin kirista dake kasar nan dasu dinga yin amfani da matsayinsu wajen dabbaka zaman lafiya da hadin kan kasa. Buhari ya yi kiran ne a babban taron karo na ashirin da uku na majami’ar Presbyterian dake kasar nan da aka gudanar a ranar asabar data gabata a a garin Kalaba. Shugaban wanda shugabar ma’aikatan tarayya ta wakilce a wurin taron uwargida Winifred Eyo-Ita, Buhari ya yi nuni da cewar akwai bukatar dasu zage wajen yin wa’azin day a shafi zaman lafiya a kasar ananmusamman ganain cewar zaben kakar 2019 yana kara karatowa. Acewar sa, taron yana cike da dinmin tarihi ganin yadda majami’un a kasar nan suke bayar da muhimmiyar gudunmawa don ci gaba da dorewar kasar nan. Shugaba Buhari ya kara da cewa, kuna bayar da mahimmiyar gudunmawa wajen daukaka ilimin zamani da fanin kiwaon lafiya da kuma hada kan alummar kasar nan. Yaci gaba da cewa,“ina yabawa majami’ar akan yadda take zuba jari akan masana’antu da ilimin zamani ta hanayar kafa shirin Presby Guest House da kuma kokarin da suke yi akan kammala jami’ar su ta Hope Waddell da nufin amfanin matsa na baya masu tasowa. Har ila yau, Buhari ya kuma yabawa mahukuntan majam’ar akan gudunmawar da suke bayarwa akan fanin noma ta hanayar gonar su mai suna Presby da kuma ta Yakurr. Ya yi amfani da damar taron, inda yayi kira ga daukacin ‘yan kasar nan dasu ci gaba da baiwa gwamnatin goyon baya akan shirye-shiryen tad a kuma yaki da cin hanci da rashawa don dora kasar nan akan turba mai dorewa. Limamin majami’ar Simila babban Rabaran Nzie Eke, ya bayyana cewar taron ya hadada sake sabunta abinda majami’ar take son cimma buri akai da kuma sama da haka, inda ya kara da cewar majami’ar zata kuma nemi tallafin kudi don kammala aikin ta na jami’ar da zai lakume naira biliyan daya da kuma akikin na Presbyterian Guest House wanda shi kuma zai lashe naira miliyan 950.Ya shawarci mabiyan majami’ar dasu shiga harkar siyasa domin su taimaka wajen samar da canjin da ake nema a kasar sun kuma tabbaatr da sun mallaki kadin sun a zabe. Acewar sa, “ ya kamat muiwa shugabanni addua’a musaman shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma fatan gudanar da zaben kakar 2019 a cikin lafiya. Ya kara da cewa, “ ina son in yi amfani da wannan damar wajen jan hankalin ku wajen mallakar kattin zabe domin ta hakan ne kawai zaku iya zabar shugabanin da suka dace.” Shima a nashi jawabin mai baiwa shugaban kasa shawara ta musamman akan ayyukan majalisar kasa Sanata Ita Enang, ya yi nuni da cewar kalubalen rashin tsaro ba kasar nan bace kwai take fama ba. Enang ya yi nuni da cewar ka da majami’ar ta yi tunanin cewar rikicin dake aukuwa a kasar nan ba wai na addini bane domin irin hakan yana aukuwa a jihar Zamfara wadda mafi yawan alummar jihar Musulmai ne. A karshe yace Nijeriya a zaman tan a kasa tana tunanin yin amfani da yarjejeniyar kungiyar ECOWAS ta jigilar kaya wadda ta baiwa bakin haure damar shigowa cikin kasar. . Copyright @leadershipayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Shugaba Buhari Ya Bukaci Coci Su Rinka Wa’azi akan hadin Kan Kasa
Shugaba Buhari Ya Bukaci Coci Su Rinka Wa’azi akan hadin Kan Kasa
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjTeqY3dcWy9vnMbi2S6RFq7mYyRyn5pkpg6HfP3zwbk_zEL7sUdRBcvQywQwviv45zrcTtyyaMlj0TIW0maedGL-UNh80ngHnXBfno5srpuW04wYqx6B8AqpV0Ia0sNE-bpLR7AkE-30TN/s320/Junaid-Mohammed-tell-buhari.jpeg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjTeqY3dcWy9vnMbi2S6RFq7mYyRyn5pkpg6HfP3zwbk_zEL7sUdRBcvQywQwviv45zrcTtyyaMlj0TIW0maedGL-UNh80ngHnXBfno5srpuW04wYqx6B8AqpV0Ia0sNE-bpLR7AkE-30TN/s72-c/Junaid-Mohammed-tell-buhari.jpeg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/shugaba-buhari-ya-bukaci-coci-su-rinka.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/shugaba-buhari-ya-bukaci-coci-su-rinka.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy