Blog Archive

Powered by Blogger.

Na Saci Mashin Ne sabo da Biyan Kudin Haya

Rundunar ‘yan sandar Jihar Nija ta samu nasarar cafke wani mutum bisa zargin sa da sace babur kusa da babbab asibitin Suleja cikin karamar h...


Rundunar ‘yan sandar Jihar Nija ta samu nasarar cafke wani mutum bisa zargin sa da sace babur kusa da babbab asibitin Suleja cikin karamar hukumar Suleja dake Jihar Nija. Shi dai wanda ake zargi sunan sa Celestine Eze dan shekara 32, wanda ya sace wa Ibrahim Gajere Fadama Suleja babur din sa kirar Bajaj. An labarta cewa shi dai wanda ake zargi yana tsaya ne a filin asibiti kafin jami’an ‘yan sanda su kama shi. Majiyarmu ta tabbatar mana da cewa a ranar Talata ne wanda ake zargin ya shiga cikin asibitin tare da nuna cewa shi majinyaci ne. Bincike ya nuna cewa shi dai wanda ake zargi ya fito ne daga Abuja kusa da filin jirgin sama sai ya zo Suleja ya aikata wannan laifin. Wanda ake zargin ya bayyana wa manema labarai cewa dalilin da ya sa ya saci wannan babur shi ne domin in biya kudin hayan gidana. “Abubuwa sun cakude min, har takai ga ban iya biyan kudin hayan gidana, gashi kuma babu aiki kota ina, ga matsaloli sun yi min yawa saboda haka na yanke shawara da in yi sata, gaskiya abu bane mai kyau,” inji shi. Shi dai wanda ake zargi ya fito ne daga kuda maso gabas na kasar nan inda ya ce “tun lokacin da na zo cikin garin Abuja nake ta fadi tashi domin in samu aikin da zai rufawa kai na asiri amma kuma aikin bai samu ba, sai ma al’amura suka kara jagulewa, sai fara tunanin kamar na yi babban zunubi a kan kaddarata, in ba barawo bane amma yanayin yadda na tsinci kaina shi ya sani sata.” Kakakin rundunar ‘yan sanda Muhammad Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, in ya kara da cewa in samu nasarar amso babaur din daga wajen wanda ake zargi. Abubakar ya ci gaba da cewa idan sun sama binciken lamarin za su muka shi zuwa kotu. Ana Bincikar DPO Saboda Cin Hanci Sashin dake kula da manyan laifuka na rundunar ‘yan sanda dake Yaba ya fara gudanar da bincike bisa zargin cin hanci da ake yiwa DPO mai kula da sashin Pen Cinema mai suma Harrison Nwabuisi. Majiyarmu ta bayyana mana cewa, DPO tare da wandasu jami’an ‘yan sanda ana zargin sune da amsar na goro daga wajen mazauna unguwar Alimi Ogunyemi dake Ijeiye. Shi dai Nwabuisi ya karyata amsar kudin belin, ba kamar yadda mazauna unguwar suka nace a kan suna biyan kudin ga shi DPO. Wakilinmu ya labarta mana cewa a ranar Laraba ne shi Nwabuisi ya jagoranci ‘yan sanda suka je wannan unguwa suka kama mutane ba tare da laifin komi ba. Sun dai kama mutane guda 37 tare da neman sai an ba su kudin beli a kan naira 15,000 ga kowannan su. Wani jami’a mai suna Bigi ana zargin ya amsa naira 30,000 ga mutane guda uku da aka kama. Kwamishinar Jihar Legas Edgal Imohimi ya dakatar da DPO, sannan ya nada jami’an da zai gudanar da binciken lamarin. Mataimakin kwamishinan na Yaba DCP Yetunde Longe shi ne zai jogoranci binciken. Wani wanda al’amarin ya faru a gaban idanonsa mai suna Ibrahim Aranjure ya ce, DCP ya tutube shi a ranar Litinin, ya kuma kara da cewa ya ziyarci ofishin ‘yan sanda tare da mutane uku. Ibrahim shi dai dan’uwan ne ga Sheriff wanda aka kama tare da mutane uku, inda aka bukaci sai sun biya naira 30,000 kudin beli. Ya ce “DCP ya wahalatta damu sasai kuma mu bamu yi laifin komi ba. Lokacin da muka isa ofishin ‘yan sanda da misalin karfe 11 na safe, duka ‘yan sandar da suka yi kaman suna cikin ofishin sanda muka isa, mun gane guda uku daga cikin harda Bigi wanda ya nemi sai an biya 30,000 a kaina sannan DPO yana cikin ofishin. “Lokacin da muka isa ofis domin ba da bayani, daga baya muka shiga ofishin mataimakin kwamishina mun hadu da DPO da kuma Bigi ido da ido. “Dukkan su sun musanta amsar kudi daga hannunmu, na yi bayani cewa na bawa Bigi kudi sannan shi kuma ya mika su ga DPO sai ya saka su a cikin aljihunsa. DPO sai ya ce, ta ya ya za a yi kudi naira 30,000 su shiga aljihu, na yi kokarin yin jayayya da shi sai DCP ya yadda. “Ni ne kadai shaida domin babu kowa sanda na ba shi kudin. Wani wanda ya biyo mu zuwa ofishin ya tabbatar da cewa Bigi ya amsa kudi cikin dare. Mutumin ya kara da cewa Bigi ya ki yarda a yi masa ta hanyar lantarki, ya ce sai dai tsabar kudi.” Wakilinmu ya bayyana mana cewa DPO yana zargin Ibrahim da ba da shaidan karya a ofishin ‘yan sanda. Rahotan ya bayyana cewa sannannen abu ne ba wani mai gaski a ofishin ‘yan sanda a kan mutanan da suka kama wanda suke neman sai an ba su kudi. “DPO ya zarge ni da yi masa karya, ni kuma na tabbatar ba karya nake yi ba. Na fada cewa DPO ya amsa kudi a kan idona amma kuma ya musanta hakan. “Lokacin da DCP ya tambaye shi yaushe aka saki wadanda aka kama sannan kuma way a sake su, sai ya kasa ba da amsa. Ya kuma kara tambayansa wadansu tambayoyi sai ya kasa ba da amsa,” inji Ibrahim. Majiyarmu ta labarta mana cewa wadansu daga cikin wanda aka kama da dare a kan lamarin ba a kai su ofishin ba. Wani mutum mai suna Nnaemeka Ogun ya gaya ma manema labarai cewa ya biya naira 4,000 a kan dan aikinsa. “An cewa masa sai ya biya naira 4,000 kudin beli a ofishin ‘yan sanda kafin a saki dan aikina wanda aka kama, wannan shi ne dalilin da ba a kai shi ofishin ‘yan sanda na Pen Cinema,” inji shi. Wani wanda abin ya faru da shi ya rubuta a shafinsa na sada zumunta na istagima cewa “in dai kana unguwar Ogba to lalle ba za ka taba kubuta daga hannun ‘yan sanda na Pen Cinema ba, yadda aka yi kenan har na shiga hannu wadannan mutane a ranar Juma’a, suka ce in yi belin kaina da kudi naira 10,000 ko kuma in zauna a wajen su har zuwa Litinin. Na kaci kaina a kan kudi naira 8,000 tare da ruko.” . Copyright @leadershipayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Na Saci Mashin Ne sabo da Biyan Kudin Haya
Na Saci Mashin Ne sabo da Biyan Kudin Haya
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgRZ0h6zKVSDh8gmtIha13pG4_wjZgo1tQ3bx23-bxDAZev423FsOwwpxVbJCxL9ngc8rOlQZgkdUZLS2ME-w0eZX6_7Pdnw-1fu2NO83Pz0Bo4kN6HiX6kNgjX5ayWBNOqQSQSix5G3pva/s320/6753565_2765796211881598179542002298543976591305522n_jpg15497b6366601552c1115822ffddf0c0.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgRZ0h6zKVSDh8gmtIha13pG4_wjZgo1tQ3bx23-bxDAZev423FsOwwpxVbJCxL9ngc8rOlQZgkdUZLS2ME-w0eZX6_7Pdnw-1fu2NO83Pz0Bo4kN6HiX6kNgjX5ayWBNOqQSQSix5G3pva/s72-c/6753565_2765796211881598179542002298543976591305522n_jpg15497b6366601552c1115822ffddf0c0.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/na-saci-mashin-ne-sabo-da-biyan-kudin.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/na-saci-mashin-ne-sabo-da-biyan-kudin.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy