Blog Archive

Powered by Blogger.

Allah ba zai yafe min ba in na goyi bayan Atiku – inji Obasanjo

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya sake nanata matsayinsa na cewa ba zai taba goyon bayan tsohon Mataimakinsa Atiku Abubakar ya ...


Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo, ya sake nanata matsayinsa na cewa ba zai taba goyon bayan tsohon Mataimakinsa Atiku Abubakar ya zama Shugaban kasa ba, inda ya shaida wa jaridar Premium Times cewa Allah ba zai yafe masa ba, idan ya goyi bayan Atiku ya zama Shugaban kasar. Cif Obasanjo ya ce, matsayinsa a kan Atiku ba zai taba canjawa ba. “Yaya zan kasance a gefen Atiku. In yi me? Idan na goyi bayan Atiku kan wani abu Ubangiji ba zai taba yafe min ba. Idan na yi haka cikin rashin sani wannan daban. Amma a ce ina sane, Atiku ba zai taba samun goyon bayana ba. Ba magana ce ta yi aiki ko rashin yin aiki tare da wani ba. Idan kana aiki ne domin inganta Najeriya ba za ka damu da wa kake aiki ba,” inji Obasanjo. Ya kara da cewa: “Akasarinku ba ku fahimci yadda nake abubuwa ba, kuma na dauka jaridarku za ta fi sanin haka. Na san Atiku sosai, kuma na sha bayyana matsayina kan Atiku. Matsayina ban canja ba. Idan ’ya’yana suna yin aure yakan turo wakilansa. Idan ’ya’yansa suna yin aure ni ma ina tura wakilai. Wannan harkar rayuwa ce ba siyasa ba. Amma a fagen siyasa matsayina bai canja ba.” “Idan na goyi bayan Atiku kan wani mukamin siyasa fiye da wanda na goyi bayansa a baya, lokacin da ban san shi ba, ba laifi, amma yanzu da na san shi, Ubangiji ba zai yafe min ba,” inji shi. Obasanjo da Atiku sun zo gadon mulki tare inda Atiku ya zama Mataimakin Shugaban kasa a 1999. Sun fara tafiya kamar abin arziki kafin su babe bayan da Cif Obasanjo ya zargi Atikun da tafka muguwar almundahana. A kwanakin baya ne Atiku Abubakar ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben badi a karkashin Jam’iyyar PDP, kuma bayan haka ne aka gan su tare da Obasanjo, lamarin da ya sa wadansu suke ganin kamar sun sasanta ne. A martanin da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya mayar ga tsohon shugaban nasa Cif Olusegun Obasanjo ya bukaci Obsanjo ya je ya gyara tsakaninsa da Ubangijinsa maimakon jingina abin da ya shafi tsakaninsa da Ubangiji kana bin da ya shafi Atiku. A martanin da ofishin kamfe din Atiku ya mayar ga Obasanjo a ranar Asabar ta bakin kakakin ofishin, Segun Sowunmi, ya ce: “Sananne ne cewa Mai girma tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, yana girmama tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo, kamar yadda yake girmama duk wani shugaban a Najeriya.” Sanarwar ta ce Atiku kuma yana girmama Obasanjo kan dalilai biyu wati kasancewarsa tsohon Shugaban kasa na biyu sun kuma yi aiki tare, wanda hakan ne ya sanya bai son ya rika mayar da martani gare shi. “To amma lura da abin da Obasanjo yake nufi cewa Ubangiji ba zai yafe masa ba in ya goyi bayan Atiku. Ina jin wannan matsala ce ta tsakaninsa da Ubangijinsa, kuma ya kamata ya yi amfani da sauran shekarunsa wajen gyara dangantakarsa da Ubangijinsa ne maimakon jingina hisabinsa a wurin Ubangiji kana bin da ya shafi Atiku,” inji Sowunmi. Kakakin ya kara da cewa, babu abin da za a jefa a kan hanyar Atiku da zai firgita shi ko ya tsoratar da shi ya gaza yin abin da ya sanya a gaba. “Ya nuna irin wannan jarumta ta zai iya fuskantar duk wani kalubale kuma ya tsaya kyam. Don haka a yayin wannan sabuwar tafiya akwai bukatar Olusegun Obasanjo ya sake tunani kan matsayinsa ya koma ga abin da akasarin ’yan Najeriya suke so, wanda a ra’ayina a ciki dukan masu son tsayawa takarar Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fi so gogewa da iya dimokuradiyya, kuma yana da hangen nesa da tsarin da zai yi aiki da ya dace da bukatun Najeriya,” inji shi. Ya kara da cewa, “Za mu ci gaba da yi wa Obasanjo fatar alheri, kuma muna shaida wa duniya cewa gaskiyar magana idan Obasanjo yana bin dokokin addininsa na Kirista zai fahimci cewa Ubangijin da yake sa ran zai yi masa hisabi ba zai so ya zama har abada shi ne kadai mai gaskiya ba, ban da sauran mutane. Ya samu amincewar jama’a, don haka saura ma za su samu. Don haka Obasanjo zai zamo abokin gaban kansa ne kawai idan ya ce zai yi gaba da kowa.” . copyright @leaderayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Allah ba zai yafe min ba in na goyi bayan Atiku – inji Obasanjo
Allah ba zai yafe min ba in na goyi bayan Atiku – inji Obasanjo
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh-_Y5aRHwWTQ6DHSJEZNLpL4uErPE4eRA5bC7SgWWF-sUhlw_3HWUax4WliPIXuifCXqc87AoMmckKoKeWpIVu3IXv3AToq9jEhyTdUXQVsXYJmeGr6euTtCbnX89KZT5IEUoLmxej1lrD/s320/obasanjo-Atiku.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEh-_Y5aRHwWTQ6DHSJEZNLpL4uErPE4eRA5bC7SgWWF-sUhlw_3HWUax4WliPIXuifCXqc87AoMmckKoKeWpIVu3IXv3AToq9jEhyTdUXQVsXYJmeGr6euTtCbnX89KZT5IEUoLmxej1lrD/s72-c/obasanjo-Atiku.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/allah-ba-zai-yafe-min-ba-in-na-goyi.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/allah-ba-zai-yafe-min-ba-in-na-goyi.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy