Blog Archive

Powered by Blogger.

Shugaba Buhari ya ce zai daure barayi da yawa a Nigeria

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban abin da zai sa a gaba bayan komawarsa kasar daga hutu shi ne daure barayi. Shugaban ya bayya...


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce babban abin da zai sa a gaba bayan komawarsa kasar daga hutu shi ne daure barayi. Shugaban ya bayyana haka ne a hirarsa da gidan talbijin na NTA ranar Asabar jim kadan bayan ya isa fadar shugaban kasar da ke Abuja, babban birnin kasar. Da aka tambaye shi game da abin da zai sa a gaba bayan ya yi hutun kwana goma, Shugaba Buhari ya ce "za mu daure barayi da dama wadanda suka jefa mu cikin matsin tattalin arziki. Da ma na san ana sa ran zan yi hakan, kuma zan yi." Yaki da cin hanci da rashawa na cikin manyan abubuwan da Shugaba Buhari ya yi alkawarin aiwatarwa lokacin da yake yakin neman zabe. Gwamnatin Shugaban na Najeriya ta gurfanar da manyan jami'an tsohuwar gwamnatin Goodluck Jonathan a gaban kuliya, inda ake zarginsu da sace kudaden gwamnati. Sai dai jam'iyyun hamayya da wasu masu sharhi na zargin Shugaba Buhari da daure 'yan adawa kawai. A cewar su, yawancin jami'an gwamnatinsa da 'yan jam'iyyar APC mai mulki na da hannu a zarge- zargen cin hanci amma ba a dauki matakin hukunta su ba. 'Yan kasar da dama na son Shugaba Buhari ya daure duk mutumin da aka samu da hannu wajen taba lalitar gwamnati ba tare da sani ko sabo ba. Shugaban na Najeriya ya ayyana sha'awarsa ta sake tsayawa takara a zaben 2019, kuma masu sharhi na ganin kalaman nasa ka iya yin tasiri wurin sake zabensa. . Copyright @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Shugaba Buhari ya ce zai daure barayi da yawa a Nigeria
Shugaba Buhari ya ce zai daure barayi da yawa a Nigeria
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhKOsnBhJjRi8wQtvSGecxNXZgGKwuvZiWhNjempfagE4acWw14TTKuHoS7Yn0BmiAv-Lz5XdCCnq-FJrcMj4asP7HcnG333csHr9NToKErHNJP3DTNCt-Az3Dp9hcWbrJ67vqjg4hy6q0k/s320/President-Miuhammadu-Buhari.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhKOsnBhJjRi8wQtvSGecxNXZgGKwuvZiWhNjempfagE4acWw14TTKuHoS7Yn0BmiAv-Lz5XdCCnq-FJrcMj4asP7HcnG333csHr9NToKErHNJP3DTNCt-Az3Dp9hcWbrJ67vqjg4hy6q0k/s72-c/President-Miuhammadu-Buhari.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/shugaba-buhari-ya-ce-zai-daure-barayi.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/shugaba-buhari-ya-ce-zai-daure-barayi.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy