Blog Archive

Powered by Blogger.

Amfanin Man Zaitun ajikin Dan Adam

Shi dai zaitun itaciyace mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan-Adam , kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, k...


Shi dai zaitun itaciyace mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan-Adam , kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninta a cikin Alkur’ani mai girma. Haka kuma kamar yadda aka samu daga Hadisan Manzon Allah (S.A.W). An karvo daga sayyadina umar yana cewa, Manzon Allah (S.A.W) ya ce kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafashi a jikinku, domin haqaqa shi yana daga cikin bishiya mai albarka. Daga Cikin Aikin Zaitun Ciwon Ciki Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya haxa da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma. Yasa mu kamar sati xaya yana sha ko kina sha, in sha Allahu zai bari. CIWON KAI Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali xaya da safe da rana da dare. Ciwon Haqori Duk mutumin da yake ciwon haqori sai ya samo ganya zaitun da ‘ya’yan habbatussauda ya saka su a cikin garwashi ya buxa bakinsa hayaqin ya dinga shiga. Ciwon Hanta Duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali xaya da safe xaya da rana xaya da dare. Ciwon Dasashi Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi. Ciwon Sukari Duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana haxawa yana sha kafin ya kwanta bacci. Ciwon Asma Duk mutumin da wannan ciwon ya kamashi, to sai ya samu ganyen zaitun ko ‘ya’yansa ya dinga turara wa. Ciwon Koda Duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a rana. Ciwon Baya Duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwava ya dinga shafawa a bayan. Ciwon Rama Duk mutumin da yaga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku, in sha Allahu zai yi qiba. Zazzavi Mai Zafi Duk mutumin da ya kamu da zazzavi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali xaya sannan yana karanta Ayatul kursiyyu sau 7 yana tofawa a cikin yana shafe jikinsa dashi. Kyawun Fuska Duk mutumin da yake so fuskar sa tayi kyau, tayi fari wanda bazai cutadda shi ba, to ya dinga shafa man zaitun da man habbatussauda in zai kwanta bacci bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo zai yi mamakin yadda fuskarsa zata koma. Zubewar Gashi Duk maccan da gashinta baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zuve, to sai ta samu ruwan zafi ta wanne kanta da shi sannan bayan ya xan huce saita zuba man zaitun a hannunta, sai ta shafe kannata da shi gaba xaya kullum. Karancin Jini Duk mutumin da yake da karanci jini a jikinsa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a rana. Bayan Gida Mai Kauri Duk mutumin da yake shan wahala in ya zo zai yi bayan gida, wani ma sai yayi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwava sai ya tura shi a cikin duburarsa. Ciwon Mara Ga Mata Duk matar da take haila tana fama da ciwon mara saboda fitar jini in tana so ta samu saukin wannan ciwon, sai ta samu man zaitun tana haxawa da ruwan tsamiya tana sha, in sha Allahu duk lokacin da zata yi haila bazai mata ciwo ba. Sanyin Qashi Duk mutumin da qashinsa yayi sanyi baya iya motsa shi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha yana kuma ya shafawa a wajan. Kyawun Fata Da Laushinta Duk mutumin da yake so fatarsa ta yi laushi da kyau, to sai ya sami man ya dinga shafe jikinsa da shi bayan yayi wanka da ruwan dumi, zai yi mamaki yadda fatarsa zata koma. Qurajen Qarzuwa Duk mutumin da yake da qarzuwa ko wasu quraje, to sai ya samu ganyan zaitun ya kirva shi ya haxa da garin habbatussauda yana shafawa a wajan har ya warke. Ciwon Kunne Duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya bari in zai kwanta bacci sai a dinga haxa man zaitun dana habbatussauda yana digawa a kunnensa. Cutar Kyasfi Duk mutumin da yake da kyasfi a jikinsa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe, ya daka shi yayi laushi sai ya hada shi da man zaitun ya cakuda, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta bacci. Shafar Aljanu Duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun saboda aljanu basa son shi. Da haka yana da kyau mutum ya lazimci amfani da shi a kowane hali, in da hali ma ya mai da shi mansa na shafawa. Ciwon Karkare Duk mutumin da ciwon karkare yasa meshi, to sai ya samu man zaitun, sannan a samu lalle a kwaba, sai a zuba man zaitun din a cikin lalle a gauraya, sannan a karanta (Ayatul Kursiyyu) sau 7 a tofa a ciki sannan sai a tofa a jikin wannan karkare. Ciwan Nono Duk matar da take fama da ciwan nono, to ana hada man zaitun da garinsa, a barbada akan nonon saboda samun damar zuba, dan kofofin su bude. Ciwon Saifa Duk mutumin da yake ciwan saifa, sai ya hada man zaitun da garin habbatussauda da kuma farar saka ya sha. Tsutsar Ciki Duk mutumin da yake da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaba su ya sha, wannan tsutsar zata mutu. Ciwan Hanji (Ulcer) Duk mutumin da yake da gyanbon ciki, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cokali daya sannan ya samu garin (kumasari)da ganyan zaitun mai laushi ya jika su ya dinga sha har sai ya warke. Fitsarin Kwance Duk yaro da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun da na habbatussauda a zuba a nono a dinga bashi yana sha zai daina. Mutuwar Jiki (Kasala) Duk mutumin da jikinsa yake yawan mutuwa to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda zai ji karfin jikinsa. Yawan Zazzabi Duk mutumin da yake yawan yin zazzabi, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cikin ludayi ya kwaba da ruwan zafi, da kuma zuma mara hadi ya dinga sha. Cuwon Gabobi Duk mutumin da gabobinsa suke ciwo to sai ya samu garin habbatussauda da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a gabobi. Kwarkwata Duk matar da take fama da kwarkwata kuma har take son rabuwa da ita, to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaba sannan sai ta bari sai rana ta take sai ta zubar wannan man a kannata ta bar shi yayi kamar minti (20) sannan sai ta wanke. TARI Duk mutumin da ya kamu da kowanne irin tari, to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da ‘yar citta da tsamiya da zuma, sai ya hada su guri daya ya cakuda ya dinga ci. Majinar Kirji Duk mutumin da yake yawan majinar kirji to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya hada ya dinga ci kullum sau biyu (2) safe da yamma. . Copyright @leadershipayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Amfanin Man Zaitun ajikin Dan Adam
Amfanin Man Zaitun ajikin Dan Adam
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEidpfh0J9nxDNoh1pLYPnOracB71G4b_bAyqwahYL6IYXjZ72AJe0gcrm9EH99q42jEyl8y5W1k6dp7mfEimIoo5R_l7A-jv-qoSAJOseCiZqfugbI3TwY86nEPrqw_XOSU2gZMtbsHqfwc/s320/Zaitun.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEidpfh0J9nxDNoh1pLYPnOracB71G4b_bAyqwahYL6IYXjZ72AJe0gcrm9EH99q42jEyl8y5W1k6dp7mfEimIoo5R_l7A-jv-qoSAJOseCiZqfugbI3TwY86nEPrqw_XOSU2gZMtbsHqfwc/s72-c/Zaitun.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/amfanin-man-zaitun-ajikin-dan-adam.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/amfanin-man-zaitun-ajikin-dan-adam.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy