Blog Archive

Powered by Blogger.

Yakamata duk 'Yan Nijeriya Su Goyi Bayan Buhari a zaben 2019

Kasancewar zabubbuka shekarar 2019, sai kara kusantowa suke yi an bukaci al’ummar kasar nan dasu kauda bambancin addini da na kabilanci su h...


Kasancewar zabubbuka shekarar 2019, sai kara kusantowa suke yi an bukaci al’ummar kasar nan dasu kauda bambancin addini da na kabilanci su hada kansu, su bada goyon baya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari, don ya sami ya sake jan ragamar kasar nan karo biyu,. Wani magidanci dake zaune a cikin garin Jos kuma mamba a Jam’iyyar APC, Alhaji Hassan Kwalla, ne ya yi wannan kira a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu na Jos, ya ce, Gwamnati wadda ke kan gado yanzu, ya kamara a kara ma Shugaban kasa Muhammadu Buhari karin wani wa’adi, don ya samu damar kammala dimbin ayyukan raya kasa da ya fara gabatar da su. Alhaji Kwalla, ya ce, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu gaggarumar nasara wajen aiwatar da muhimman aiyukan inganta rayuwar al’ummar kasar nan, a cikin ‘yan shekaru uku da rabin da ya yi da kama jan ragamar kasarnan wanda ya fi na shekaru goma sha-shida, da gwamnatin da ta gabata ta jam’iyyar PDP ta yi a lokacin da take kan mulki. Ya yaba ma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa bisa irin nasarorin data samu na kammala aiki a jihar Filato, ya kuma bukaceta da ta kara kaimi a kan, rarraba katuttukan jefa kuri’a don bada dama ga dimbin mutanen da suka yi rijista su sami zuwa runfunan zabe saboda su jefa kuri’a ga wanda suke so ya jagorance su. Ya nemi hukumar da ta kara wuraren da za a rarraba katunan zaben don saukake wa masu amsar katunan. Alhaji Kwalla, ya yaba a kan irin kyakkyawan hadin kai da ’yan jam’iyyar APC, suke dashi a jihar sai kuma ya bukace’su da su kara hada kansu don tunkarar zabubbukan domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a shekarar 2019. Ya yi Allah wadai da batancin da wadansu ‘yan siyasa maras kishin ci gaban al’umma suke yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari, saboda kokarin da yake yi na ganin kasar nan ta kubuta daga cin-hanci da rashawa da wadansu ‘yan kalilan mutane maras kishin kasa suka tsunduma kan su. . Copyright @leadershipayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Yakamata duk 'Yan Nijeriya Su Goyi Bayan Buhari a zaben 2019
Yakamata duk 'Yan Nijeriya Su Goyi Bayan Buhari a zaben 2019
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi68JmX8eZOP_VwFrJzDLoEUDcenCc6YOKNEgkkRoQ5JaUtsVrAsV9DrRQzaTl739DJghI4t8l-PXDQUIJU8ZwosQI-HkWldr6RppabJe5O-j1zfoA3Isn5_-Cqm3ijKXzasAlG9QdNtOIz/s320/Page-4-First-story-Shugaba-Buhari-2.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEi68JmX8eZOP_VwFrJzDLoEUDcenCc6YOKNEgkkRoQ5JaUtsVrAsV9DrRQzaTl739DJghI4t8l-PXDQUIJU8ZwosQI-HkWldr6RppabJe5O-j1zfoA3Isn5_-Cqm3ijKXzasAlG9QdNtOIz/s72-c/Page-4-First-story-Shugaba-Buhari-2.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/yakamata-duk-nijeriya-su-goyi-bayan.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/yakamata-duk-nijeriya-su-goyi-bayan.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy