Blog Archive

Powered by Blogger.

Kungiyar Matasan Arewa ta bawa shugaba Buhari wata uku ya kawo karshen kashe-kashe a Arewa

Wata kungiyar Gamayyar Matasan Arewa mai suna Arewa Youth Coalition for Peace sun nuna damuwa da gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ...


Wata kungiyar Gamayyar Matasan Arewa mai suna Arewa Youth Coalition for Peace sun nuna damuwa da gazawar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari wajen kawo karshen kashe- kashen da ake yi wa ’yan Arewa a kasar nan. A cewar kungiyar, yankin Arewa a yanzu ya zama wajen da ake kashe mutane babu gaira babu dalili. kungiyar ta kuma yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kawo karshen kisan gillar da ake yi wa mutane musamman talakawa wanda su suka zabe shi kafin nan da wata uku. Shugaban kungiyar Kwamared Muktar Muhammed ne ya sanar da haka a ganawarsa da manema labarai a Kaduna a ranar Asabar da ta gabata. Ya ce muddin Shugaban kasar ya kasa kawo karshen kashe-kashen a jihohi Zamfara da Sakkwato da Filato da Benuwe da sauransu kafin cikar wa’adin da suka bayar za su fito su yi zanga-zangar lumana sai an biya musu bukatarsu. “Bukatarmu ita ce Shugaban kasa ya kawo karshen wadannan kisan gillar da ake yi wa ’yan Arewa domin babu amfani a ce mutanen da suka zabe ka kuma yau su ake kashewa ba tare da an kare rayuka da dukiyoyinsu ba. Idan har ba a kawo karshen kashe-kashen ba za mu yi kira ga matasan kasar nan dsu kaurace wa zaben da za a yi nan gaba domin babu amfanin zaben mutumin da ba zai iya samar muku da tsaro ba,” inji shi. Don haka sai ya ce gamayyar tasu za ta ci gaba da wayar wa mutane kai su tabbatar sun zabi wanda suke da yakinin zai kare musu rayuka da dukiyoyinsu a zabe mai zuwa. “Tuni shirye-shirye suka yi nisa wajen ganin mun ilmantar da jama’a a kan abubuwan da suke faruwa. Mu abin da ya fi damunmu a yanzu shi ne wadannan kashe-kashe da ake yi a kasar nan kuma har yanzu a ce an kasa hukunta masu kashe mutane babu gaira babu dalili,” inji shi. Kwamared Muktar ya yi fatan Allah Ya kawo karshen fitinu da ke damun kasar nan. . Copyright @aminiya

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Kungiyar Matasan Arewa ta bawa shugaba Buhari wata uku ya kawo karshen kashe-kashe a Arewa
Kungiyar Matasan Arewa ta bawa shugaba Buhari wata uku ya kawo karshen kashe-kashe a Arewa
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhDt9T_79oZZyR3UZg0rfjY-gM0WFfUrP4o-PFT4vZnj94PP8KF4gptFarkR-Ill-3SBp90sbQmhuTZ7_qgwYjumikr0ihrR363-eDYeEehiZHxbFOBhUyzzXW0a9nVhFiThEIfyLEi5Nfn/s320/600x-1.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhDt9T_79oZZyR3UZg0rfjY-gM0WFfUrP4o-PFT4vZnj94PP8KF4gptFarkR-Ill-3SBp90sbQmhuTZ7_qgwYjumikr0ihrR363-eDYeEehiZHxbFOBhUyzzXW0a9nVhFiThEIfyLEi5Nfn/s72-c/600x-1.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/kungiyar-matasan-arewa-ta-bawa-shugaba.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/kungiyar-matasan-arewa-ta-bawa-shugaba.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy