Blog Archive

Powered by Blogger.

Ni Ban damu da ficewar wasu daga APC ba – inji Shugaba Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu abin da ya dame shi da masu ficewa daga jam’iyyarsa ta APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP ...


Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babu abin da ya dame shi da masu ficewa daga jam’iyyarsa ta APC zuwa jam’iyyar adawa ta PDP da sauran jam’iyyu. Shugaba Buhari ya sanar da haka ne a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da yake amsa tambayoyi daga ’yan Najeriya mazauna kasar Togo, a birnin Lome. Kakakin Shugaban kasar, Garba Shehu ne ya bayyana haka a ranan Litinin, a cikin wata takarda da ya fitar a Abuja. Ya ce Shugaba Buhari ya ce bai damu ba, saboda ’yan Najeriya suna da kyakkyawan yakini a kan gwamnatinsa, kuma suna yaba muhimman ayyukan da yake yi da kokarin da yake yi. “Ina tabbatar muku cewa mafi yawan ’yan Najeriya can a gida suna yaba aikin da muke yi,” inji Shugaban kasar. Da yake nuna farin cikinsa, kan yadda dandazon ’yan Najeriya mazauna Togo suka taru daga yankunan kasar biyar domin ganawa da shi, Shugaba Buhari ya yi murna da yadda suke ba shi labarin irin gagarumin ci gaba da ya samar a Najeriya. Wannan ya nuna lallai, suna kasar Togo da zama, amma zukatansu suna Najeriya. Haka Shugaban ya shaida musu cewa da a ce gwamnatocin baya sun yi amfani da kashi 25 bisa 100 na kudaden danyen man fetur, to da Najeriya ba za ta yi kukan komai ba a halin yanzu. Ya buga misali da Dala biliyan 16 da aka salwantar wajen kokarin farfado da wutar lantarki, amma ba a samu wutar ba, sai ma karin duhu. Sannan sai ya yi musu alkawarin cewa za a sayar da dukan duk kadarorin da aka kwato daga hannun wadanda suka wawure su, sannan a sanya kudin cikin baiti- malin Najeriya. . Copyright @aminiya

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Ni Ban damu da ficewar wasu daga APC ba – inji Shugaba Buhari
Ni Ban damu da ficewar wasu daga APC ba – inji Shugaba Buhari
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiuwMoDqiXs2IaLMtD4JIyeVR96Vl_HpWMzj57QtSKCkL14nt5924EAVxoixceh6lXyzruAreQ3LcdeC-34rEQf8a7f3EhcBZ7y3XcQPB2A4poYR1sE7_v-DBFR9uhyphenhyphenl8h8LOU2PuoqE_p-/s320/600x-1.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEiuwMoDqiXs2IaLMtD4JIyeVR96Vl_HpWMzj57QtSKCkL14nt5924EAVxoixceh6lXyzruAreQ3LcdeC-34rEQf8a7f3EhcBZ7y3XcQPB2A4poYR1sE7_v-DBFR9uhyphenhyphenl8h8LOU2PuoqE_p-/s72-c/600x-1.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/ni-ban-damu-da-ficewar-wasu-daga-apc-ba.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/08/ni-ban-damu-da-ficewar-wasu-daga-apc-ba.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy