Wani dan shekata 45 wanda kuma ya kammala makaranta baya da aikin yi mai suna Tijiro Oghenede dake yankin Ozoro a cikin karamar hukumar Isok...
Wani dan shekata 45 wanda kuma ya kammala makaranta baya da aikin yi mai suna Tijiro Oghenede dake yankin Ozoro a cikin karamar hukumar Isoko ta Arewa ciki jihar Delta, ana zargin ya kashe kansa saboda kasa biya wa matar sa kudin gadon asbiti don a sallame ta daga asibitin. An ruwaito cewar,Tijiro asibitin ya bashi takardar biyan kudin ne Naira 250,000 da asibitin ya duba lafiyar ta a cikin yan watannin da suka shige,inda wannan yawan kudin ya chaza masa kai a daren ranar alhamis data gaba, musamman ganin cewar tun lokacin da ya kammala jami a shekaru bakwai da suka shige bai samu aikin yi ba. DSP Aniamaka Andrew, kakakin rindinar yan sandan jihar ne ya tabbatar da hakan a hirar da da kafar Daily Post a garin Asaba, inda ya kara da crwar, Tijiro ya kashe kansa ne a ranar lahadin data wuce atar sa asibitin ne a ranar lahadin data wuce bayan da yan uwan sa suka tafi Coci kuma an samu gawar sa ce a cikin dakin sa har da kwayoyina kusa da gawar. Ya kara da cewa Tijiro Oghenede ya kulle kofar dakin ne sannan ya kashe kansa,inda saida aka balle kofar. Majiya kusa da yan uwan marigayin ta bayyana cewar Tijiro tun kusan watanni uku da suka shige yaki yin barazanar son kashe kansa saboda bai.samu aikin yi ba kuma ya kasa ciyar da matar sa. Sai dai, kanin sa mai suna Earnest Oghenede ya bayyana cewar, “yaya na yaki zuwa gona ya yi aiki kuma kaddara ya je ya yi aure alhali bai da aikin yi shi ne ya je ya sha magunguna da suka wuce iyaka ya mutu. An ruwaito cewar,Tijiro Oghenede ya roki mahukuntan adibitin akan su bar shi ya dauki matar sa ya kai ta gida tare da yi masu alkawarin zai dinga biyan su kudin su a hankali a hankali, amma suka ki yarda. copyright @hausaleadership
COMMENTS