Blog Archive

Powered by Blogger.

Ni kadai Zan Kara Da Buhari Na Kada Shi A 2019 –inji Turaki

A karshen makon nan ne Alhaji Kabir Tanimu Turaki dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP ya sha alwashin cewar shi ne z...


A karshen makon nan ne Alhaji Kabir Tanimu Turaki dan takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP ya sha alwashin cewar shi ne zai dauki Buhari sama ya nana a kasa a zaben da ke tafe na dubu biyu da sha tara, yake cewa zai samu wannan nasarar ne a sakamakon kasa-kasau da Buhari ya yi wajen cika alkawuran da ya dauka wa jama’an kasar nan. Turaki wanda shi ne Dan Masanin Gwandu (SAN) ya bayyana hakan ne a wajen wani taron tuntuba da ya kawo zuwa sakatariyar jam’iyyar PDP a jihar Bauchi, inda ya bayyana cewar gwamnatin APC ta shirya manyan karerayi wajen mallakar zukatan ‘yan Nijeriya a zaben 2015 inda ya bayyana cewar kawo yanzu jama’an Nijeriya sun gamsu karya aka shirya musu. A bisa haka ne ya bayyana cewar mafitar kasar nan tana hanunsu, inda ya sha alwashin gudanar da nagartaccen shugabanci idan aka zabesu a zaben 2019 da ke tafe. Kabir Tanimu ya ce, “Zaben 2015 APC sun zo da karerayi da yawan gaske; suka ce mu ‘yan PDP barayi ne, suka ce bamu da maganin kawo karshen rikicin Boko Haram; an yaudari ‘yan Nijeriya da karya da farfaganda. Yau an wayi gari a Nijeriya ana cewa ba haka aka so ba. “Mu ‘yan PDP yanzu muna shirye mu fitar da ‘yan Nijeriya daga halin kakanikayi da ukuba da aka jefa kasar nan a ciki. An kakaba wa ‘yan Nijeriya talauci, yunwa da rashin abun yi, uwa- uba ga matsalar kashe-kashen jama’a da ya addabi wasu sassan kasar nan a halin yanzu,” Inji Dan Masanin Gwandu Ya kara da cewa, “’Yan Nijeriya sun san abubuwan alkairan da jam’iyyar PDP ta yi a shekaru 16 da take mulki, muna shirye yanzu idan muka dawo mulki mu daura muhimman aiyuka fiye da wanda muka taba yi. Kura-kuran da muka tafka za mu kiyaye idan muka dawo,” In ji Turaki Turaki ya yi zargin cewar gwamnatin APC ta yi siyasa da harkar tsaro, inda ya bayyana cewar da badin shigar da siyasa cikin lamarin tsaro ba, da kawo yanzu an shawo kan matsalolin, “Gwamnati tana bayar da makuden kudade wa ‘yan Boko Haram ta hanyar da bashi ne mafita ba. wannan yana basu zarafi suna sake sayen makamai da suke kai hari wa jama’a,” In ji shi. Turaki Dan Masanin Gwandu ya bayyana cewar matsalolin tsaro da suke ci gaba da addabuwa a kasar nan abun kunya ne ga gwamnatin Buhari, “Sun yi alkawarin cewar a cikin wata uku zasu kara da Boko Haram. Yau an wayi gari Filato, Nasarawa, Binuwai, Kogi, Adamawa, Taraba da wasu bangarorin kudu maso yamma da kudu maso gabas kashe-kashen jama’a kawai ake samu da sunan rikicin manoma da makiyaya amma wannan gwamnatin ta kasa fitowa da tsarin da zai kare rayuwa da dukiyar ‘yan kasar Nijeriya,” Kamar yadda ya shaida Turaki ya kara da cewa matsalolin tsaro sun yi katutu, don haka ne ya bayyana cewar idan ita gwamnatin ta kaza za su amshi mulkin kasar domin shawo kan wannan matsalolin da suke addabi Nijeriya, “A maimakon gwamnati ta dauki ‘yan sanda dubu 30 ta aike da su dajin Zamfara ko Binuwai, a’a wannan adadin za a dauka ne akai jihar Ekiti domin a samu zarafin yin magudin zabe. Wannan ya nuna cewar gwamnatin nan bata da niyya bata da tsarin karemu,” A cewar dan takarar shugaban kasar Alhaji Kabir Tanimu Turaki ya daura da cewa Buhari ya sharara wa mutanen kasar nan karerayi masu tarin yawa don a zabe shi, “ya ce idan aka zabeshi a matsayin shugaban kasa ba zai sake zuwa kasar waje domin jinya ba, yau baya zuwa? Ya ce, zai rage farashin kudin mai an rage? Ya ce zai maida farashin dala ya zama daidai da naira, an cika alkawarin? Ya ce zai soke ofishin matar shugaban kasa ya soke? Ya ce, idan ya hau zai kawo karshen Boko Haram cikin wata uku ya yi?. To sai ya ci gaba da yi wa jama’an kasa karya,” A tabakin Turakin Turaki ya jawo hankalin ‘yan jam’iyyar PDP wajen yin duk mai iyuwa domin hada kai don fuskantar Buhari, ya bayyana cewar dole ne ‘yan PDP su hada kansu a wannan lokacin, ya bayyana cewar matsalolin rabuwan kawuka a fadin kasar nan, “In na samu nasara aka zabeni a matsayin shugaban kasa zan hada kan ‘yan Nijeriya. Lokaci yayi da ‘yan Nijeriya suke bukatar agajinmu, domin mun yi musu sun kuma gani,” Kamar yadda ya bayyana. Ya ce, lokaci ya yi da za su fatattakin gwamnatin azzaluma, “Wannan gwamnati azzaluma Allah zai kawo lokaci da za mu kwace mulki a hanun APC. Kuma da yardar Allah nine zan kwace wannan shugabancin kasar nan daga hanun Buhari,” In ji Kabir Turaki Da yake nasa jawabi, shugaban jam’iyyar PDP na jihar Bauchi, Alhaji Hamza Akuyam ya gode wa dan takaran a bisa ziyarar da ya kawo jihar ta Bauchi, Akuyam ya sha alwashin cewar nasara na tare da jam’iyyar PDP a zaben da ke tafe. . Copyright @leadershipayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Ni kadai Zan Kara Da Buhari Na Kada Shi A 2019 –inji Turaki
Ni kadai Zan Kara Da Buhari Na Kada Shi A 2019 –inji Turaki
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgITCmRvXu_dZ_XqqWiygCq5BoJid6ykAKgPnF3gHXIEpM8Q6Jbzauiob0dYHqcksU-L44_-7sAzIaRsBjefbFpkdoAYnscywWzk9sNQ3Q_SOmu8AYIJZYqVH3pF6m5IJ3JwUYYJOo3i8Ib/s320/turaki-640x640.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgITCmRvXu_dZ_XqqWiygCq5BoJid6ykAKgPnF3gHXIEpM8Q6Jbzauiob0dYHqcksU-L44_-7sAzIaRsBjefbFpkdoAYnscywWzk9sNQ3Q_SOmu8AYIJZYqVH3pF6m5IJ3JwUYYJOo3i8Ib/s72-c/turaki-640x640.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/ni-kadai-zan-kara-da-buhari-na-kada-shi.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/ni-kadai-zan-kara-da-buhari-na-kada-shi.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy