Blog Archive

Powered by Blogger.

Hanyoyin da zakibi domin gyara fatar jikinki

Assalamu Alaikum tare da fatan ana lafiya. Kowa ne abu a rayuwarmu na bukatar gyara. Yadda yana da kyau mu tsaftace muhallinmu haka kuma yak...


Assalamu Alaikum tare da fatan ana lafiya. Kowa ne abu a rayuwarmu na bukatar gyara. Yadda yana da kyau mu tsaftace muhallinmu haka kuma yake da mahimmanci mu tsaftace jikinmu. Duk kyaun mutum idan har babu gyaran fatar jiki, lallai kyaun baya bayyana. Shi yasa masu magana suka ce idan kana da kyau sai ka kara da wanka. Ganin hakan ne ya sanya ni na kawo muku hanyoyi daban-daban wadda za’abi domin gyaran fatar jiki. • Hadin kurkum da lemun tsami; a hada garin kurkum da ruwan lemun tsami da nono cokali daya sannan a kwabasu a guri daya sai a rika gogawa a fatar jiki da na fuska na tsawon mintuna biyar sannan a bar hadin ya tsumu a jiki na tsawon mintuna ashirin kafin a wanke. • Nono da garin bawan lemun zaki; a shanya bawan lemun zaki har sai ya bushe sannan a daka a tankade a zuba nono kadan a kwaba da shi sannan a shafa a fuska na tsawon mintuna ashirin kafin a shiga wanka a kullum. • Ruwan lemun tsami da nono; a kwaba ruwan lemun tsami da nono a guri daya sannan a shafa a fuska ko jiki na tsawon mintuna ashirin kafin a wanke. Yana da kyau a gwada wannan hadin a fatar hannu idan har baiyi wa fatar illa ba na tsawon mintuna goma, za’a iya amfani da shi a jiki baki daya. • Zuma; A daura zuma a wuta idan ya dan yi dumi sai a shafa a fuska a bari ya tsumu na tsawon mintuna ashirin kafin a wanke da sabulu. Yin hakan na kashe kwayoyin cutar dake haifar da fesowar kuraje. • Man zaitun da gishiri; a zuba man zaitun a cikin gishiri sannan a rika murza hadin a fuska na tsawon mintuna biyar kafin a wanke domin cire fatar da ta yi saba a fuska da jiki. • Ruwan kwa-kwa; a markada kwa-kwa sannan a matse ruwar jikinta sai a riga shafa ruwan a fuska da jiki na tsawon mintuna biyar kamin a wanke a kullum domin samin fata mai santsi. • Ruwar kal tuffa; a sami kal tuffa sannan a shafa ruwansa akan kurajen fuska da auduga a bari ya bushe na tsawon mintuna biyu zuwa uku. • Zuma da ruwan lemun tsami; a kwaba ruwan lemun tsami da zuma sannan a rika shafawa a fuska domin kashe cutukan fuska da kuma dada mata haske tare da samin santsin fata. . Copyright @aminiyya

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Hanyoyin da zakibi domin gyara fatar jikinki
Hanyoyin da zakibi domin gyara fatar jikinki
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEikFoMFU8nn81dI4npFcJkvnCpQSaDff54pIwidfAvfKWm4Mq4Tw_LN2oBLRf2Bg4mO_gJ2f6tGx6iafK30NvkrnBOADqN3w7EarbPwYMA-vmadWwTAejuhTbjOZWSroaGFaBFJRqtZYQxY/s320/www.alummata.com_pear.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEikFoMFU8nn81dI4npFcJkvnCpQSaDff54pIwidfAvfKWm4Mq4Tw_LN2oBLRf2Bg4mO_gJ2f6tGx6iafK30NvkrnBOADqN3w7EarbPwYMA-vmadWwTAejuhTbjOZWSroaGFaBFJRqtZYQxY/s72-c/www.alummata.com_pear.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/hanyoyin-da-zakibi-domin-gyara-fatar.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/hanyoyin-da-zakibi-domin-gyara-fatar.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy