Hakora na daya daga cikin abubuwa da ke fitar da kyawun mace. Don haka ya kamata a ba su kyakkyawar kulawa. Wadansu matan sukan shiga halin ...
Hakora na daya daga cikin abubuwa da ke fitar da kyawun mace. Don haka ya kamata a ba su kyakkyawar kulawa. Wadansu matan sukan shiga halin takura, inda ko an yi abin dariya sai su rufe bakinsu da hannu kafin su yi dariya, saboda halin da hakoransu suka samu kansu a ciki. A wannan makon mun taho miki da hanyoyin da za ki yi amfani da su wajen lura da hakoranki. Ga abubuwan da ya kamata ki yi da kuma wadanda za ki gujewa don samun lafiyayyen hakori. Abubuwan Da Za Ki Yi Amfani Da Su 1. Za ki iya amfani da jus din lemun tsami ko kuma ruwan lemun tsami wajen cire dabbare-dabbaren da ke cikin hakora. Idan lemun tsami ne sai ki yanka sannan ki matse ruwan, daga nan sai ki kurbi ruwan, sannan ki kuskure bakinki. Za ki iya amfani da hannunki wajen cuccudawa. 2. Idan kina so hakoranki su yi fari, kuma abin sha’awa sai ki samu ‘ya’yan itacen Strawberries, sai ki yayyanka daga nan sai ki yi buroshi da su. 3. Idan kika goge hakoranki da ruwan lemun zaki ma yana sanya hakora su yi haske. 4. Idan akwai datti ko dabbare-dabbare a hakoranki sai ki samu gishiri ki kuskure bakinki da shi. Ki dangwali gishiri da yatsanki sannan ki cuccuda hakoranki. 5. Cin ‘ya’yan itatuwa da alayyahu na cire dabbare-dabbare a hakori. 6. Ki samu buroshin goge baki sai ki dangwali sinadarin hydrogen perodide sannan ki goge hakoranki da shi. 7. Idan kin ci abinci sai ki goge bakinki, hakan zai sanya hakoranki su yi kyau da kuma sheki. Abin Da Ya Kamata Ki Gujeshi Domin Samun Lafiyar Hakora – Ki guji yawan shan abubuwan da ke dauke da sinadarin carbon (Carbonated drinks), wadannan abubuwan shan suna dauke da sinadarin acid din da ke kashe hakora sannan yana sanyasu su samu dabbare-dabbaren. – Ki guji yawan shan kofi (Coffee) ko Nescafe domin suna sanya hakora su yi duhu. – Ki guji yawan cin goro ko shan sigari domin suna dauke da sinadarin nicotine da ke kashe hakora da kuma sanya hakora su yi duhu. – Ki guji yawan shan zobo yana bata hakora. . Copyright @leadershipayau
COMMENTS