Blog Archive

Powered by Blogger.

Gwamnatin Shugaba Buhari ta fi ko wacce cin hanci – inji Atiku

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya bayanna gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari a matsayin wacce ta fi kowace cin hanci tun...


Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya bayanna gwamnatin Shugaba Muhamadu Buhari a matsayin wacce ta fi kowace cin hanci tun bayan da kasar ta koma kan tafarkin mulkin dimukradiyya a shekarar 1999. Alhaji Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Talata a garin Abakaliki lokacin da ya ke yi wa magoya bayan jam'iyyar PDP bayani a ofishinta na jihar Ebonyi. Ya je jihar Ebonyi ne domin ya ci gaba da neman goyon bayan 'yan jam'iyyar PDP don 'zama dan takarar shugaban kasa' a jam'iyyar a 2019. Ya ce abu daya da jam'iyyar APC mai mulki ta ke alfahari da shi shi ne yaki da cin hanci da rashawa, sai dai ya ce yaki da rashawa ba shi kadai ne alhakin da ya rataya a wuyan gwamnati ba. "Abin da ke faruwa yanzu shi ne kasarmu na sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulki, ya kamata a ce muna da gwamnati da ta kunshi kowa da kowa amma kun san cewa wannan gwamnati ba ta kowa da kowa ba ce," in ji shi. "Kun san babu hadin kai a cikin wannan gwamnati, kun san gwamnati ce da ta gaza, kun san cewa gwamnati ce da fi ko wacce cin hanci tun bayan da kasar ta koma kan tafarkin mulkin dimukadiyya a shekarar 1999. "A kan haka, ka da ku yadda wani ya zo ya yaudareku kan cin hanci da rashawa. Sun fi ko wacce gwamnati da na sani cin hanci tun bayan 1999, kuma za mu fasa kwai dangane da yadda suke cin hancin da rashawa. "Yaki da rashawa ba shi kadai ba ne alhakin gwamnati,." in ji Atiku. Alhaji Abubakar ya fadawa taron jama'a cewa ya zo jihar ne domin ya nemi goyon bayansu, domin kayar da shugaba Buhari a 2019. Ya ce gammayar da jam'iyyar PDP da kuma wasu jam'iyyu 37 suka kafa shi ne mataki na farko na kayar da shugaban kasa a zaben da za a yi a badi. A lokacin da ya tarbe shi, Gwamna David Umahi na Ebonyi ya ce 'yan yankin kudu maso gabashin Najeriya za su tattauna kan zaben shugaban kasa na 2019, kuma za su zabi dan takarar da zai kawo wa yankin ci gaba. . Copyright @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Gwamnatin Shugaba Buhari ta fi ko wacce cin hanci – inji Atiku
Gwamnatin Shugaba Buhari ta fi ko wacce cin hanci – inji Atiku
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgifpsZCA91-_uwAw2_FJhveOvCfT_57MnT1fpaSW97RVSP2BRWfFRa05L4GL4GpwOJCe-tb3fb3zlgAwOz1XAAqPjMFclRZt47TnTRB0SC9omCv2aE7I6oVDs_bawB2Rrr1Zd990c0L4AT/s320/atiku-abubakar-20191.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgifpsZCA91-_uwAw2_FJhveOvCfT_57MnT1fpaSW97RVSP2BRWfFRa05L4GL4GpwOJCe-tb3fb3zlgAwOz1XAAqPjMFclRZt47TnTRB0SC9omCv2aE7I6oVDs_bawB2Rrr1Zd990c0L4AT/s72-c/atiku-abubakar-20191.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/gwamnatin-shugaba-buhari-ta-fi-ko-wacce.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/gwamnatin-shugaba-buhari-ta-fi-ko-wacce.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy