Blog Archive

Powered by Blogger.

Ni Ban iya karatu da sauri ba – inji Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya karbi bakuncin takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa. Shugaba Buhari ya bai wa masu sukarsa ...


Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya karbi bakuncin takwaransa na Afirka ta Kudu, Cyril Ramaphosa. Shugaba Buhari ya bai wa masu sukarsa wata kafa wadanda suke kiransa "Baba mai tafiyar hawainiya" bayan ya amince cewa ya kasa sa hannu kan yarjejeniyar yin kasuwanci ba tare da shinge ba na nahiyar Afirka, saboda "ba ya iya karatu da sauri." Shugaba Buhari ya ce yana da aniyar sa hannu kan yarjejeniyar da shugabannin Afirka suka rattaba hannu a kai a kasar Rwanda a watan Maris, nan ba da jimawa. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ruwaito cewa a taron manema labarai da aka yi a ranar Laraba, Shugaba Buhari ya ce: "Ina son na tabbatar an ci ga da samun guraben ayyukan yi da kayayyaki a cikin kasarmu, ya kamata mu yi taka tsan-tsan kan yarjeniyoyin da za su sa a rika gogayya da watakila samun nasara kan masa'antunmu masu tasowa." "Ba na iya karatu da sauri, watakila saboda ni tsohon soja ne. Ban karanta yarjejeniyar cikin sauri ba, kafin jami'aina suka ce ya kamata na sa hannu. Ya kara da cewa "Na ajiye takardar kan taburina. Kuma zan sa hannu a kai nan ba da jimawa ba." Shugaba Buhari na magana ne lokacin da shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kai ziyara kasar. Tun farko Mista Ramaphosa ya fada wa 'yan kasuwa 'yan Najeriya cewa akwai wurare da dama da kasarsa za ta amfana daga yarjejeniyar kasuwanci ba tare da shinge ba, kuma ana kan nazari kan daftarin doka da zai ba mutane damar zirga-zirga daga wani yanki zuwa wani yanki. Wannan ita ce ziyarar Mista Ramaphosa ta farko zuwa Najeriya tun bayan da ya zama shugaban kasa a watan Fabrairun da ya gabata. Ya ce kasar Afirka ta Kudu na son ta karfafa alakar da ke tsakaninta da Najeriya. Kasashen biyu su ne suke da tattalin arziki ma fi girma a Afirka. . Copyright @bbchausa

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Ni Ban iya karatu da sauri ba – inji Buhari
Ni Ban iya karatu da sauri ba – inji Buhari
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgMHmXLDoBsYmh97NogOXG0r7Gj3OFMnV3a_kaSlUY2qXKLOcQzSy66lvHN2qIZq7jM66EU1mcaM6gtBW3rOZ2ZMcPhnPws1P7D3MOc5-FcsxquTzJroyEU2BqVqp4OoEYdj7YjzhGNncpl/s320/32713937-1634698479961909-7706809970716573696-n.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgMHmXLDoBsYmh97NogOXG0r7Gj3OFMnV3a_kaSlUY2qXKLOcQzSy66lvHN2qIZq7jM66EU1mcaM6gtBW3rOZ2ZMcPhnPws1P7D3MOc5-FcsxquTzJroyEU2BqVqp4OoEYdj7YjzhGNncpl/s72-c/32713937-1634698479961909-7706809970716573696-n.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/ni-ban-iya-karatu-da-sauri-ba-inji.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/ni-ban-iya-karatu-da-sauri-ba-inji.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy