Blog Archive

Powered by Blogger.

Makircin Shaidanu/Aljannu Ga 'Ya'ya Mata

Ya ‘yan’uwa masu karamci, mu sani Allah (SWA) ya gargade mu sosai ya ja kunnan mu a kan cewa shi iblis da rundunar sa aljannu, makiyanmu ne ...


Ya ‘yan’uwa masu karamci, mu sani Allah (SWA) ya gargade mu sosai ya ja kunnan mu a kan cewa shi iblis da rundunar sa aljannu, makiyanmu ne na asali da za mu guje su, mu koma zuwa ga Allah (SAW). Akwai wacce ta samo Bayahuden Aljani a wurin ‘party’ a Kaduna, kuma iyayenta suna kallon ta ta shirya ta tafi waurin ‘party. din, sun sa kaya masu kyau masu bayyana kwalliya da jiki. To sai ya kasance inda aka haya, a kai Fatin din, wuri ne da aljanu daga sassa na duniya suke zuwa suke yin taron su na tsaface-tsafacen su, saboda su a cikin aljanun ma ‘yan ‘Sikiret Society ne, saboda haka, a lokacin da ‘yan biki suka zo suna ta casar rawa da kade-kade, shi ne kawai daya daga cikin manyan aljanun Yahudawan nan ya ga wannan yarinyar, nan da nan ya afka mata nan take ma sai da ya yi amfani da ita. Ya kuma kira mutansa nan take aka daura masu aure da ita, kuma ya sa wasu daga cikin bayinsa aljanu su dinga gadinta har su dari, a lokacin ba ta gama Makarantar Sakandare ba. Saboda haka duk manemin da ya matsa a kan aurenta, kashe shi suke yi, kuma sukan daure ta irin daurin Yahudawa. Wani lokaci a same ta tsirara ba ko wando, sun kuma daddaure ta tamau, har sukan daga ta sama, alhalin tana daure kuma tsirara, duk wannan azabar yana mata ne wai don kada ta yi magana da wani mutum, wato yana kishi kenan. Haka su kai ta yawon neman magani shekara biyar ba su gajiya ba, inda har Allah (SAW) Ya kawo su wurin mu, sai muka fara yi musu aiki. Aljanun nan suke ta shigo mana da yaudara mai yawa, amma Allah (SAW) Ya taimake mu a kansu, sai da mu kai kwana Arba’in muna abu daya kullum, a karshe wannan aljanin ya dauki biro da takarda ya yi mana rubutu irin nasu, ya bamu cikakken labarin yadda abin ya faru da kuma cewa har ma sun haifi yara uku da ita. Kuma ya rubuta wasu fa’idoji na magani masu yawa, ya ce, ga shi nan toshiyar baki ne, kuma idan na yarda zai kawo min kudi masu yawa, don in kara jari, ko da ‘Dollars na ke so. Kuma duk abin da ya rubuta na tanbaye ta, ta ce gaskiya ne, don haka mu ka ci gaba da yi mata aiki har Allah (SAW) Ya ba ta cikakkiyar lafiya har ta yi aure. Ya ‘yan’uwa, idan muka lura gabadaya, wannan abin da ya faru cutarwar aljanu ne da makircinsu ga dan adam, tun daga kan iyayen da suka kasa tsawatar da ‘ya’yansu da kuma auren da za a yi, maimaikon a godewa Allah, sai ka ga an gina fati, har da rawa da kade-kade da nuna tsiraici ga Mata da ma Mazan. Kuma shi tsiraici haramun ne nuna shi, sai ga wanda ya halatta, Allah (SAW) Ya ke cewa a cikin Kur’ani Mai girma; “Kul lil Mu’uminina yah fizu min absarihim, wa yah fizu furujahum, zalika azka lahum innal Laha khabirun bi ma yasna’una.” “Kul lil Muminina, yagzuzna min absarihinna, wa yahfazna furujahunna, wala yubdina zinata hunna illa ma zahara minha.” Wato Allah (SWA) Yake cewa Manzon Allah (SAW) ka cewa Muminai su dinga kauda kansu, kar su dinga kallon tsiraicin mata, kuma su kare kansu kar su bayyananar da al’aurarsu, kuma kar su yi zina, domin yin hakan shi zai zama tsarki a gare su, Allah (SWA) lallai shi mai bada labarin abin da mutane suka aikata ne. Allah (SWA) Ya ci gaba da cewa: “Ka ce wa muminai Mata su ma su dinga kauda kansu kar su dinga kallon tsiraicin wasu, kuma su kama kansu, kar su bayyanar da al’aurarsu, kuma kar su yi zina, kuma kar su bayyanar da kwalliyarsu, sai abin da ya bayyana a kan ba yadda za su yi. Ya ‘yan’uwa idan muka lura Allah (SWA) Ya ce mu dinga kauda kai kar mu dinga kallon tsiraicin juna, to shi Iblis da shi da rundunarsa, aljanu da yake suna da ilimi sun san wadannan ka’idoji, kuma sun san amfanin su, ma’ana yadda ya zo a cikin tafsirin, Kurdabi da Ibni Kasir: karkashin Suratul Bakara, FadinSa, “Illa iblisa aba, wastakbara wa kana minal kafirin.” Wato iblis ya yi girman kai, shi ne Ikrima da Sa’alaba suka samo ruwaya daga Ibn Abbas yake cewa, ‘ai iblis abin da ya sa shi girman kai, shi ne, saboda Allah (SAW) Ya sa shi cikin Mala’iku kuma aka ba shi ilimi kusan ya fi na su, wato shi yana da tarin ilimi mai yawa. To saboda wannan ilimi da su aljanu suke da shi, to shi ya sa sai suka yi kaidi iri-iri, to shi ya sa suka kawata wa mata cewa, su bayyanar da kwalliyar su kuma su dinga fito da tsirincinsu ana ganin bayansu yana kadawa da kirjinsu yana rawa da gashinsu a waje yana sheki. Shi kuma aljani ya zauna a duwannan ta da mamanta yana kawata ta ga duk wanda ya kale ta, kamar yadda ya zo a hadisin da Bukhari ya fitar. To tunda kusan duk mata haka su ke yawo, ka ga kenan kau da ido zai yi wahala, saboda in ka kauda shi gefen dama sai ka ga wata mace ta bayyanar da jikinta, to can ma hagun wata za ka gani wata kala ta fi ta daman, haka in baya ka kalla ko gaba, kai ta kallon kasa kuma, wata ta zo da Nonuwanta ta bangaje ka, tun da matan yanzu ba su fiya kaucewa maza ba, saboda sha’awa da tai masu yawa. Kuma aljanu sun hana su aure, ko kuma ka je ka bangaje ta, da Duwawu duk dai sharri ya same ka wanda ya fi na baya. Saboda haka, sai dai mutum ya kulle idonsa yanda sakamakon in bai yi hankali ba, ya je ya fada rami ko mota ta kade shi, saboda haka, sakamakon wahalar da kare kai daga kallon tsiraci yake da shi a wannan lokaci namu shi ya sa sha’awa take yi wa maza yawa. Saboda wata ma matar aure ce, amma za ta bayyanar da jikinta matukar bayyanarwa, sai ya sa mazan su yi iya kokarin su ta kowacce hanya su ga cewa sun yi amfani da wannan macen, ko kuma wacce tsautsayi ya fada kanta, wa iyazu bil Lah. Allah ya kare mu. Kuma wani mugun kaidi da aljanu suke amfani da shi, kamar yadda wata mace ta bayyana min, kuma mu ka bincika, mu ka samu yana faruwa a kan mata da yawa. Shi ne, a lokacin da Namiji ya je wurin Mace, sai Aljani ya taso da sha’awarta da tsanani. Saboda da haka, Namijin a nan, latsawa kadan zai yi, sai gabadaya ta fita daga hayyacinta, ta koma kamar Mahaukaciya, nan take shi ko in ya so ya yi amfani da ita zai yi. Don wata ma, sai bayan an gama, sai ta zauna ta kama kuka. Matar take cewa, ita har a gama ma ba ta san abin da yake faruwa ba, sai dai tana jin dadi matsananci, fiye da wani dadin. Manzon Allah (SAW) da ya ke Allah Ya ba shi ilimomi masu yawa na sanin abin da yake a boye, ko da ko mu ba ma ganin abin, sai ya ce, “Duk sanda Namiji ya kebe da Macen da ba Muharramarsa ba, to na ukunsu Aljani ne.” kamar yadda ya zo a cikin littafin, Mu’ujamul Kabir, na Imamu Dabarani. Allah (SWA) muke roko da ya kawo mana agajinsa, amma wannan irin siffar kaidi na wadannan Aljanun mai girma ne, sun yi kokarinsu na hana yin aure, ta hanyar munanan Mata, su sa ta, ta bayyanar da kwalliyarta a waje wanda Aljanu ne suka sa masu wannan a zuciya. Suka ce masu za a fi ganin su sosai, sai a aure su. Su kuma suka aikata haka, ga shi kuma Aljanun sun ki yarda a aure su, sai dai su na sa wa ana ta fasadi, kuma suna ta kashe wa matan aure ta hanyoyi daban-daban. Ga shi kuma Manzo Allah (SAW) ya ce, “Idan wani daga cikinmu, ya ga matar da ta birge shi, har ya yi sha’arwarta, to ya je ya biya bukatarsa a wurin matarsa.” Kamar yadda Muslim da Tirmizi suka fitar daga Jabir (RA) ya ke cewa, “Watarana suna zaune a wurin Manzon Allah (SAW), sai wata mace ta zo, saboda haka Manzon Allah (SAW) yana dago kai sai ya ganta, saboda haka sai ta darsu a zuciyarsa, a take ya tashi ya shiga cikin gida yaje ya biya bukatarsa a wurin Zainab bintu Jahash, sai ya fito har ga ruwa yana digowa daga kansa na wankan da ya yi, sannan ya ce, da sahabansa, Wato ita mace idan ta fito a wannan siffar aljanu a gaban ta da bayanta. Saboda haka, duk wanda ya ga wata mace da ta burge shi, to ya tafi wurin matarsa ta gida. To yanzu halin da ake ciki, Matan, Aljanun sun hana su aure, ballantana Mijinsu idan ya ga wata na waje ta ba shi sha’awa, ya taho wurin ta. Haka su ma Mazan, Aljanu sun hana su aure, ballantana in sun ga wacce ta tayar masu da hankali su koma gida don su biya bukatarsu. Wato dukkansu sun hadu da, ‘ta’adilul zawaj,’ wanda kuma dole sai an magance ta. Fahimta Fuska Assalamu Alaikum. Malam, ni ne nake zargin wani mutum da wata matar aure, zan iya fadawa mujinta? Haramun ne ka fadawa mujinta, haramun ne ka fadawa wani kuma haramun ne ka bincika don tabbatar da gaskiyar al’amarin ko abin da ake yin zargin a kai din. Don haka babu ruwanka da yin wani bincike a kai, ko tattauna al’amarin tare da wani ko wani abu makamancin haka, kawai ka kyale su. Allah Ya sakawa Malam da alheri. Wallahi ina da sha’awa sosai, sannan kuma aurena sai nan da shekaru biyu. Malam, me ya kamata na rika yi? Abin da za ka rika yi shi ne, sanya lemon tsami a abicin da za ka ci. Kazalika, abin da ya sa kake jin haka, saboda sabuwar balaga ce da kuruciya; amma duk da haka kada ka damu za ka wuce wannan lokacin. Assalam Malam. Don Allah a taimaka min, ina so na bar zina amma abin ya gagara na kasa dainawa, don girman Allah a taimake ni. To, babban abin da ya kamata kuma hanya mafi sauki shi ne abu uku, na farko ka nace da yin ibada yadda ya kamata, ka tabbata cewa, Sallolin nan biyar kana yin su a jam’i, sannan ka rika zuwa minti ashirin ko sha biyar kafin a tayar da Sallah, ka yi nafila raka’a biyu ko hudu kafin Sallar azahar ko bayan an idar ko ka je Sallar la’asar ka yi Sallah raka’a biyu ko hudu kafin liman ya zo, ko ka je Sallar magriba minti talatin kafin liman ya zo ya kuma ci gaba da istigfari kafin liman ya zo, sannan bayan an idar da Sallar magriba din ka rika yin Nafila raka’a shida. Haka zalika, ka fin Sallar isha’i, ka je da wuri ka yi Sallar raka’a biyu, bayan an yi isha’I ka yi shafa’I da wuturi ko kuma ka yi nafila raka’a biyu idan ka je gida ka yi shafa’I da wuturin. Sallar asuba kuma ka je da wuri kafin a kira assalatu, mana’a dai ka jajirce wajen yin wadannan Salloli biyar a jam’i. Abu na biyu kuma, ka ci gaba da jin cewa, abin da kake aikatawan nan ba daidai ba ne kuma ka rika jin haushin kanka da abokiyar zinan taka sannan ka rika rokon Allah gafara. Abu na uku kuma, ka yawaita yin ayyukan alheri, kamar azumi, sadaka da kyauta da sauran duk wani abu da ka san Allah yana so daidai gwargwadon ikonka, insha Allahu Allah zai yaye maka. Haka nan ka daure ka yi aure, idan z aka yi auren kuma ka auri irin matar da ka fi sha’awa. Salam. Malam, don Allah idan mutum ya sa yi abu a hanya ya manta bai biya kudin ba, shi ma wanda ka sayi abun a wajen sa bai tuna ya tambaye ka kudin ba sai bayan ka yi gaba sannan ka tuna ka dawo amma ba ka same shi ba saboda yawo yake ga shi kuma ba Musulmi ba ne, Malam, ya kenan za ka yi da kudin? Sai kawai ya yi masa sadaka da kudin, Allah Ya san ta inda zai mayar wa mai kudin kudinsa. Idan kuma daga baya sun hadu, ya mayar masa da kudinsa ladan sadakar kuma yawo wajensa. Assalam. Malam, na kasance mai yawan yin sadaka da kyauta amma sau da dama maigidana yakan yawan yi min fada a kan hakan, Malam, idan nay i bai sani ba akwai matsala? Idan da dukiyarsa kike yin wannan kyauta da sadaka tunda bay a so, ki daina yi masa kyauta da dukiyarsa, amma idan da dukiyarki kike yi, a nan dole za ki rage yi sosai ta yadda ba zai ji ba kuma ba zai rika gani ba. Idan kika yi haka babu shakka za a samu zaman lafiya a tsakanin ku. Assalam Malam. Idan mutum ba shi da lafiya, ba zai iya azumi ba sai ciyarwa, maimakon ya ciyar da safe da yamma da kuma dare, zai iya bayar da kwanon masara ya wadatar, ko kuwa sai ya hada da kudin cefane? A’a, mutum zai iya bayar da mudu daya na masara ko dawa ko gero ko wake ko kuma shinkafa mudu daya tak ba kwano ba kamar yadda wasu ke fada. Amma idan yana da hali babu laifi idan ya hada da kudin cefane. . copyright @leadershipayau

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Makircin Shaidanu/Aljannu Ga 'Ya'ya Mata
Makircin Shaidanu/Aljannu Ga 'Ya'ya Mata
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhwbhd_DxuLUQMEPCD9AwA6vefHbS7LYXvX1gvqQNAxGyEoeGSkZH4At0nd8d9twM5Q66VuqdT0CoGjStdhUGqzCp693-l7tOH2IUyOwKxImqdRiDx4g52wVdk06Zmv4tJ1UOFrVnLqmEl3/s320/images_3.jpeg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEhwbhd_DxuLUQMEPCD9AwA6vefHbS7LYXvX1gvqQNAxGyEoeGSkZH4At0nd8d9twM5Q66VuqdT0CoGjStdhUGqzCp693-l7tOH2IUyOwKxImqdRiDx4g52wVdk06Zmv4tJ1UOFrVnLqmEl3/s72-c/images_3.jpeg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/makircin-shaidanualjannu-ga-mata.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/07/makircin-shaidanualjannu-ga-mata.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy