Wani bawan Allah mai suna Garba Dahiru, ya gina Kabari ya na kwana a cikinsa kowane dare, saboda tsoron Allah. Shi de Garba Dahiru mazaunin...
Wani bawan Allah mai suna Garba Dahiru, ya gina Kabari ya na kwana a cikinsa kowane dare, saboda tsoron Allah.
Shi de Garba Dahiru mazaunin unguwan Yakubu Wanka
ne, cikin garin Bauchi, ya ce tsananin tsoron Allah
ne da zaman Kabari ya sa ya gina kabari kusa da dakinsa yake kwana kullum a ciki.
Garba ya shaida wa manema labarai haka ne a
garin Bauchi da ya ke ba da bayanai akan dalilan
da yasa ya maida Kabari wurin kwanansa.
Kamar yadda gidan Jaridar Aminiya ta ruwaito
labarin, Garba ya ce yana haka ne domin neman gafara da tuna Mahaliccinsa.Ya ce yakan shiga ne
kullum, yau Sama da shekara biyar Kenan.
malam garba dahiru yace Gaskiya idan na shiga na fito ina gyara wasu
laifuffukana sosai, don haka nake jin dadi sosai.
“Sannan idan na zo fita daga cikin gidana, nakan
dauka idan na dawo kawai za a kawo ni cikin kabarin nan ne.
“Wannan shi ne abin da nake sanyawa a cikin
raina, ina ganin kamar za a kawo ni a matsayin
matacce ne, tunda Allah bai ce ga lokacin da zan
mutu ba, amma dai na san kowane rai mamaci ne.
Garba ya kara da cewa yakan kuma bari ne sai dare ya yi sosai sannan ya shiga kamar karfe biyu zuwa
uku sai ya shiga ya kwanta a ciki.
“Idan na shiga cikin kabarin nakan kwanta ne sai
in rika surantawa a raina kamar na mutu ne ina
cikin kabari.
.
Allah yasa mu cika da imani
COMMENTS