Shahararren jarumin nan kuma furodusa Zaharadeen Sani ya ce ya samu amincewar hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS tare da hukumar tantance fi...
Shahararren jarumin nan kuma furodusa
Zaharadeen Sani ya ce ya samu amincewar
hukumar ‘yan sandan farin kaya DSS tare da
hukumar tantance fina finai ta kasa domin ya
shirya fim da ke nuna rikicin Boko Haram.
A wata hira da yayi da jaridar Premium Times, Zaharadeen ya ce ya fuskanci kalubale da
farko domin hukumar tantance fina finai ba ta
amince da fim din ba saboda irin tufafin ‘yan
ta’addan da aka yi amfani da su da kuma
bindigogi da khakin sojoji.
Ya ce haka kuma ya samu gayyata daga DSS domin ya zo ya kare dalilansa na shirya fim
din.
Zaharadeen ya ce ya shirya fim din ne saboda
ya nunawa mutane illar da rikicin Boko Haram
ya haifar a kasar nan, wanda da shi ne yake
kwana da shi yake tashi. Fim din mai suna ABU HASSAN dai ana
hasashen cewa ba a taba yin irin sa ba a
Kannywood.
Labarin ya nuna wata kungiyar ta’addanci da
ta addabi mutane wacce sojoji suka ci
lagwanta daga karshe. Za’a fara Nuna wannan shiri a film House
cinema dake Kano a ranar 27/10/2017.
COMMENTS