Blog Archive

Powered by Blogger.

Zargin Da Ake Min Na Karbar Cin-hanci Ba Gaskiya Ba Ne – inji Ganduje

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karyata zargin da ake yi masa na karbar na goro ko toshiyar baki daga wasu kamfonin da ke aikin...


Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karyata zargin da ake yi masa na karbar na goro ko toshiyar baki daga wasu kamfonin da ke aikin kwangiloli da aka zargi Gwamnan da karbar toshiyar baki ko na goro kamar yadda Jaridar Daily Nigeria ta fitar da wasu faya fayen bedio da ke nuna cewa mai girma Gwamnan Kano ya karbi na goro daga wasu kamfanonin kwangila a Jihar Kano. Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karyata haka ne alokacin da ya gurfana a gaban kwamitin dake bincike wanda Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa karkashin jagorancin Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dakta Baffa Babba Dan Agundi. Gwamna wanda Kakakin Gwamnatin jihar Kano kuma kwamishinan yada Labarai Malam Muhammad Garba ya wakilta, ya bayyana cewa wannan zargi karya ne babu wannan magana, kasancewar Gwamnan Kano tsohon ma’aikaci ne kuma an san tarihinsa, kuma ba a sanshi da irin wannan harka ta karbar cin-hanci da rashawa ba kamar dai yadda shi kwamishinan yada labaran na Jihar Kano Malam Muhammad Garba da ya wakilci Gwamna agaban Kwamitin dake bincike akan zargin karbar na goro kamar yadda aka saki faya-fayen bedio daga waccen Jarida Daily Nigeria da Jafar Jafar ke shugabanta. Shi dai kwamitin ya gayyaci Gwamna ne domin bada ba’asi akan al’amari kamar yadda amakon da ya gabata suka gayyaci Jafar Jafar dan Jaridar da ya fara sakin wannan faifai na bedio da ake zargin Gwamna Ganduje kan wannan al’amari. Kwamishina Malam Muhammad Garba da yake amsa tambayoyin manema Labarai a kan wannan lamari ya bayyana cewa wannan zargi ba sabo ba ne an yi wa magabata a baya kamar Sarkin Kano, tsohon Gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da dai sauran makamancin ire- iren wannan zargi na bata suna, wanda kuma ba wani abu bane illa iyaka siyasa da kuma kusantowar zaben shekara ta 2019. Haka kuma game da rashin zuwan Gwamnan kuwa Malam Muhammad Garba ya bayyana cewa ai shi ne kakakin gwamnatin Kano kuma shi ke magana da yawun gwamnati, don haka ba wani sabon abu bane idan ya wakilci Gwamna akan kowane irin al’amari. Cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu ga manema labarai jim kadan daga fito wa daga zauren majalisar dokokin ta jihar Kano akwai Kwamishinan Ma’aikatar Shari’a na Jihar Kano Hon. Barista Muktar wanda ya bayyana cewa duk wannan abu ba za a tabbatar da laifi a kan kowa ba sai dai idan shari’a ce ta yi bincike kuma ta tabbatar da laifinsa, don haka wannan abu gaskiya ce zata tayi kanta, kuma kowa yasan Gwamna ba mutun ne wanda zaka iya cewa ya yi wani abu na saba doka ba, kasancewarsa tsohon ma’aikaci da yasan dokokin aiki da tafi da al’amuran gwamnati. Shima lauyan Gwamna Ganduje na kashin kansa Ma’aruf Yakasai ya bayyana cewa irin wannan an yi wa Malam Ibrahim Shekarau kan bude asusun ajiya akasashen waje, da aka yi bincike aka tarar abun ba gaskiya ba ne, saboda haka wannan ma gaskiya za ta yi kanta na cewa babu wannan magana ta cin-hanci da rashawa daga gwamna Kano, a cewar Barista Ma’aruf Yakasai lauyan Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Tunda farko dai sai da shugaban kwamitin Dakta Baffa Babba Dan’agundi ya bayyana cewa wannan rana ce kuma a irin wannan lakaci ne aka tsara za a zauna bayan an gayyaci Gwamnan Kano Dakata Abdullahi Umar Ganduje kuma ya amsa cewar zaizo, kuma abisa aka’ida shi ne idan gwamna ya ga damar zuwa ya zo don kare kansa akan zargi, idana kuma yaso ya turo wakilci idan ma yaso yaki amsa gayyatar baki daya, wannan shi ne abin da yake a tsari, amma rashin zuwan Gwamna ko rahsin wakilci ba zai hana kwamiti aiwatar da dukkan abin da ya kama na zartarwa a yi ba a kan wannan lamari, kuma abu ne da ya zama dole ayiwa kowa adalci a dukkan wanda abin ya shafa. Saboda haka abu na gaba za a zauna da Lauyan Gwamnati da kuma Lauyan Jafaf Jafar domin ganin wannan faifan bedio a ranar Talata 6 ga watan Nuwamba, sai dai kuma a dokar Majalisa wannan zaman a asirce ake yinsa. Wakilanmu da suka majalisar sun rawaito maa cewa wannan zaman an yi shi ne kasa da minti talatin a majalisar dokokin da ke cikin sakatariyar gwamantin Jihar Kano ranar Juma

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Zargin Da Ake Min Na Karbar Cin-hanci Ba Gaskiya Ba Ne – inji Ganduje
Zargin Da Ake Min Na Karbar Cin-hanci Ba Gaskiya Ba Ne – inji Ganduje
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgvLs93pbuornSn84NeTRRWW_CuTqo_inZmYOBusDVl5_0wHS1RYGpa9qlXwPOwre5TRHfPbE8RutLZrVkhE2uD44iOt1Rkc3z0RVwufXIofZFMOiD__0b38qp3hqUX9D1L814JuvO5mt6q/s320/GAnduje.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgvLs93pbuornSn84NeTRRWW_CuTqo_inZmYOBusDVl5_0wHS1RYGpa9qlXwPOwre5TRHfPbE8RutLZrVkhE2uD44iOt1Rkc3z0RVwufXIofZFMOiD__0b38qp3hqUX9D1L814JuvO5mt6q/s72-c/GAnduje.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/11/zargin-da-ake-min-na-karbar-cin-hanci.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/11/zargin-da-ake-min-na-karbar-cin-hanci.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy