Blog Archive

Powered by Blogger.

Tsawon Shekara Daya Mijina Bai Sadu Da Ni Ba, Me Ya Kamata Na Yi?

Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah ya samu dace. Malam don Allah ina son na san matsayin aurena shekara daya mijina be kusance ni ba al...


Assalamu alaykum. Malam ya ibada? Allah ya samu dace. Malam don Allah ina son na san matsayin aurena shekara daya mijina be kusance ni ba alhalin muna tare kuma dukkanin mu muna lafiya. Nagode Wa’alaikum assalam, Auranku ingantacce ne, amma zai yi kyau a kira magabatanku a tattauna matsalar, tun da saduwar ma’aurata ginshiki ne na Zamantakewar aure, wanda rashinsa yana kai ma’aurata zuwa saÉ“on Allah. In har ba ku cimma matsaya ba, bayan zama da magabata kina iya kai shi Kotu alkali ya muku hukunci, Saboda a musulunci bai Halatta miji ya kauracewa matarsa ba sama da wata (4) kamar yadda aya ta (226) a suratul Bakara ta tabbatar da haka. Allah ne mafi sani. Ta Haihu Kafin Ta Cika Wata Bakwai Da Aure, Mene Ne Hukunci? Assalamu Alaikum. Malam yarinya ne aka aurar da ita batayi wata bakwai ba 7 ta haihu cikakkiyar yarinya yar wata tara (9) to malam meye hukuncin auren kuma ya hallaccin jaririyar a musulunci? Wa’alaikum salam, In har an San tana da ciki aka yi auran wannan hukuncinsa a fili yake, kuma auran bai inganta ba a zance mafi inganci, amma in haihuwa ta yi Kafin ta cika wata bakwai, kuma ba’a santa da ciki ba to dansa ne, saboda ayar suratu Lukman da tá suratul Ahkafi sun nuna cewa ana iya haife ciki a watanni shida. Auran dá aka yi dá cikin shege ba tare da an sani ba ya inganta, saidai ba zá’à danganta cikin zuwa mijin ba, tunda ba shi ya yi ba.In har ya san tana da ciki bayan sun yi aure.bai halatta ya take ta ba har saí ta haihu,saboda fadin Annabi s.a.w. “Duk wanda ya yi imani dá Allah da ranar Lahira to kar ya shayar da ruwansa ga shukar waninsa” kamar yadda Abu-dawud ya rawaito. In ta haihu za su iya cigaba dá mu’amalarsu ta aure, musamman in bai sani ba saí dá aka daura. Allah ne mafi sani. Hukunce-Hukuncen Mai Takaba Assalamu alaikum wa rahmatullaah. Gafarta Malam a yi mana bayani ko da a takaice ne dangane da hukunce -hukuncen takaba. Na shiga wajen mahaifiya dazu, take cewa in tambaya mata Malamai tanadin shari’a a kan wannan al’amari. Nagode Wa’alaikum assalam To dan’uwa ina rokon Allah ya jikan mahafinku, akwai hukunce-hukunce da suka shafi takaba, ga muhimmai daga ciki: 1. Mai takaba za ta zauna a gidan mijinta ba za ta fita ba, har sai ta gama iddarta, wacce take wata hudu da kwana goma, kamar yadda aya ta: 234 a suratul Bakara take nuni zuwa hakan . 2. Ba za ta saka kaya masu kyau ba, don haka za ta guji ado, kamar yadda hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304, ya yi bayanin hakan. 3. Shari’a ta hana mai takaba ta sanya turare, kamar yadda hadisin Bukhari mai lamba ta: 5343, ya tabbatar da hakan, 4. Malamai suna cewa mai takaba ba za ta sanya tozali ba, kamar yadda hadisin Nasa’i mai lamba ta: 3565 ya bayyana hakan. 5. An hana mai takaba yin lalle, kamar yadda hanin ya zo a hadisin Abu-dawud mai lamba ta: 2304. 6. Idan wata bukata ta kama za ta iya fita daga gida, ko da rana ne ko da dare. 7. Za ta iya yin Magana da mazan da ba muharramanta ba, idan bukatar hakan ta kama, saidai ta guji, sanyaya murya, kamar yadda aya ta 32 a suratul- ahzab ta hana sanyaya murya ga wadanda ba muharramai ba. 8. Babu wani launi na kaya na musamman da aka shar’anta mata ta sanya, don haka, duk kayan da ba kwalliya a jikinsu ya halatta ta sanya su . 9. Za ta iya yin wanka da sabulun da yake ba mai kanshi ba. 10. Za ta iya zama ta yi hira da makusantanta, har ma za ta iya bude gashin kanta, idan su duka muharramanta ne. 11. Bai halatta wani ya nemi auranta ba, har sai ta gama idda, saidai za’a iya yin jirwaye mai kama da wanka, kamar yadda aya ta 235 ta yi nuni zuwa hakan. 12. Idan mai takaba tana da ciki, to iddarta ita ce: haife abin da take dauke da shi, kamar yadda hadisin Subai’a mai lamba ta: 5014 a Sahihul Bukhari ya tabbatar da hakan. Allah ne mafi sani. Kakata Ba Ta Iya Sallah Saboda Rudewa Ko Za Ta Fadi A Kanta? Assalamu alaikum ina fatan Dr. yana cikin koshin lafiya, Allah ya kara masa imani da fasaha Amin. Dr kakata ce tsufa ya kamata ga rashin lafiya, yaranta tara bata gane Ko daya daga cikin su gashi bata gane alwala b

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Tsawon Shekara Daya Mijina Bai Sadu Da Ni Ba, Me Ya Kamata Na Yi?
Tsawon Shekara Daya Mijina Bai Sadu Da Ni Ba, Me Ya Kamata Na Yi?
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgKN6c-sMcP0oJChx_FRjIN9xbDThQ4IpsbCDskOOap6ZQ6K5nGPAJsPUtnvPm1M_dQPgSjjtjlIHxMy5CHBbcZEBE2rKdXVU0ojSxKDfYBc4YOlbiN62ZIBep0ZKNKCjY8S4StfBJ9djGx/s320/Page-22-pix.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgKN6c-sMcP0oJChx_FRjIN9xbDThQ4IpsbCDskOOap6ZQ6K5nGPAJsPUtnvPm1M_dQPgSjjtjlIHxMy5CHBbcZEBE2rKdXVU0ojSxKDfYBc4YOlbiN62ZIBep0ZKNKCjY8S4StfBJ9djGx/s72-c/Page-22-pix.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/11/tsawon-shekara-daya-mijina-bai-sadu-da.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/11/tsawon-shekara-daya-mijina-bai-sadu-da.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy