Blog Archive

Powered by Blogger.

Ni MarayaNe Dana Fara Da Tallan Itace a Adamawa – inji Atiku

Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana yanda ya taso a cikin wahala a matsayinsa na ...


Dan takarar shugabancin kasar nan a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayyana yanda ya taso a cikin wahala a matsayinsa na maraya mai tallan itace a kan titunan garin Jada, da ke Jihar Adamawa. Atiku ya fadi hakan ne a sa’ilin da yake kaddamar da yakin neman zabensa ranar Litinin, inda yake magana kai tsaye a shafinsa na Twita mai adireshin, Atiku Abubakar @atiku. Atiku yana cewa. “Na taso ne a matsayin maraya mai tallan itace a kan titunan garin Jada, ta Jihar Adamawa, Allah cikin ikonSa, ta hanyar hidimar da kasar nan ta yi mani, yau ga abin da na zama. “In har Nijeriya ce ta yi mani irin wannan hidimar, ashe ya zama tilas a kaina na tabbatar da ku ma Nijeriya ta bunkasar da za ta yi maku irin wannan hidimar. Tsohon Mataimakin Shugaban kasan cikin shelanta kaddamar da takaran na shi ya ce, yanzun lokaci ya yi da za a dawo da martabar Nijeriya, yana mai cewa, “Ina rokon ku, ku zo mu tafi da ku tare wajen ganin mun gyara kasar nan.” Atiku ya ci gaba da cewa, “A yau mun fara bin hanyoyin musayar ra’ayi a kan tsare-tsaren mu na samar da ayyuka, sake fasalin tsarin, da mayar da Nijeriya a kan turban ci gaban da aka santa. “In har an zabe ni a matsayin Shugaban kasa, zan shige gaba wajen jawo ra’ayin masu zuba jari, zan kuma taimaka wa masu kanana da matsakaitan sana’o’i a cikin kasar nan, domin ganin mun ribanya kudaden ajiyarmu zuwa dalar Amurka bilyan 900 ya zuwa shekarar 2025. “Wannan jarin da za mu zuba zai iya samar da ayyukan yi akalla milyan 2.5 a duk shekara akalla za a iya fitar da mutane milyan 50 daga kangin talauci a cikin shekaru biyu. “Ni da ‘yan tawaga na, za kuma mu kirkiro ayyuka ta hanyar bullo da wasu shirye-shirye kamar na koyar da sana’o’i a kasa baki-daya, a inda za mu koyar da masu ayyukan hannu maza da mata akalla milyan guda a kowace shekara. “Shirin da nake da shi na sake fasalin kasar nan zai kai ga gagarumin karin hanyoyin samar da kudaden shiga ga gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin Jihohi, ta hanyar bayar da tallafin da ya dace ga Jihohin ta yanda za su inganta hanyar samar da kudaden shigan su. “Bari na bayyana maku a sarari, babu wata Jiha a kasar nan da za ta sami kasa da abin da take samu a halin yanzun, a bisa zahirin gaskiya ma, Jihohin za su sami kari ne a bisa abin da suke samu a halin yanzun, irin kokarin da duk wata Jiha ta yi, shi ne yanayin abin da za ta iya samu. “Ba kawai ina tallata maku wadannan manufofin nawa ne ba, so nake ku amshe su. Ku duba su da idon basira. “Za ku iya duba su a shafina mai adireshi kamar haka, http://www.Atiku.org da kuma ‘yan takardun da za mu rarraba maku su, kuma za ku sami damar tofa albarkacin bakin ku.”

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Ni MarayaNe Dana Fara Da Tallan Itace a Adamawa – inji Atiku
Ni MarayaNe Dana Fara Da Tallan Itace a Adamawa – inji Atiku
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjqRCFbGaKJfSmF_UrFb-n0a681Z1zv68DO9XA4o0_mJLMLmNVRCGFSLx45XybxA7U5ntlOzuVgLzCHxiGZySeuHePtPPauN9pyjr8na0F1MMcAyQ7WPOtGaiQOZWyTk62PY_YB_pWJUz7D/s400/Atiku-Abubakar-speaking-1.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEjqRCFbGaKJfSmF_UrFb-n0a681Z1zv68DO9XA4o0_mJLMLmNVRCGFSLx45XybxA7U5ntlOzuVgLzCHxiGZySeuHePtPPauN9pyjr8na0F1MMcAyQ7WPOtGaiQOZWyTk62PY_YB_pWJUz7D/s72-c/Atiku-Abubakar-speaking-1.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/11/ni-marayane-dana-fara-da-tallan-itace.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/11/ni-marayane-dana-fara-da-tallan-itace.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy