Blog Archive

Powered by Blogger.

Mene Ne Dalilinki Na Hana Mijinki ya Kara Aure?

yadda za su zauna cikin aminci da natsuwa, wato dai miji ake fatan ya yi ta kai kawo wajen daukan dawainiyar iyalansa. A karantarwar Addinin...


yadda za su zauna cikin aminci da natsuwa, wato dai miji ake fatan ya yi ta kai kawo wajen daukan dawainiyar iyalansa. A karantarwar Addinin Islama ta fito fili wajen tabbatar wa maza auren macce guda da kuma damar karawa zuwa mata biyu ko uku ko hudu in ya san zai iya yi masu adalci kuma zai iya kula da su, amma idan ya san ba zai iya yin adalci ba to ya auri mace daya. Allah ya hore mu a kan cewa ka da kowa ya karkata zuwa ga nuna fifiko a fili na son wata cikin matansa har ya bar dayar ko sauran matan su zama marasa amfani a cikin gidansa, wanda kowa ya tara mata amma ya ki yi masu adalci to a ranar alkiyama zai tashi sashin jikinsa a shanye. Dan haka sai mu kula da sauke nauyi matayenmu. Mu sani fa muna cikin wani zamanin da ba mai yi maka musu in ka ce mata na da matukar yawa fiye da maza, amma bisa hikimar Allah duk wannan yawan matan an yi masu tanadin wurin shiga shi ne an yarda ko wani namiji daya ya auri har mata guda hudu idan yana da hali kuma yana iya yin adalci. Madallah da wannan dama don za ta taimaka wa ‘yan uwa mata kowa ta samu mijin aure da yardan Ubangiji. Yanzu dan uwa yadda kididdigar masana ke nuna yawaitar mata, me kake tunani a nan gaba zai faru in kowani namiji ya ki aure ko ya kara aure? Kuma iyaye na mata in kuka kasa, kuka tsare, kuka toshe kofar karo aure ina makomar ‘ya’yanku ‘yan mata da kannen ku ko ‘ya’yun ku zaurawa da mutuwar aure ko mutuwar miji ya jawo mata zawarci? Annabi (S.A.W) yana cewa: Duk wanda kuka amince da addinisa da halinsa idan ya zo neman aure, to ku aurar masa. A nan ba a yi mana nuni da sai mai kudi, ko mai mulki ko wani dan boko ba, a’a mai addini da hali mai kyau ake so. In aka ki bin wannan umarni to fitina da barna mai yawa za su wanzu a bayan kasa. Ya kamata mu natsu sosai mu ga yadda rashin damar yin aure ke jefa matansan mu maza da mata cikin shaidanci da sabon Allah. Kuma haka iyaye ke zaune cikin zulumi da takaicin ganin ‘ya’yansu manyan ‘yan mata ba aure. Ga samari na ta cizon yatsa, kamar ka ce a yi masu rukiyya in suna hirar barkwanci a kan aure, har ka ga ‘yan mata tika-tika sai shafe-shafe da shiga dandalin sada zumunta na zamani ba ranar aure, har jinkiri ya sa ta fara neman maganin jinnu da shiga bokaye. Ga zaurawa nan ta ko ina, idan aka ce a yi kirgen zaurawa ne to kusan ko wanni gida akwai, ga kuma fitsararrun mata ‘yan ina da biki, abun dai sai addu’a ba dadin ji a cikin wannan zamani. Sai dai wani abin mamaki shi ne har zuwa yau al’ummarmu da shugabanninmu duk an kasa daukar matakin wannan matsala wanda tun kana jin labarin yawan mata marasa aure a can wata kasa, yanzu har ka fara hangota a hankali yau gashi ta iso garin ku ko kaima har a ce ga kanwarka, ko ‘ya’yanka ko diyarka ko wata marainiya a unguwarku a zaune ba aure ba kuma manemin auren. Da zamu nemi sanin alkaluman yawan mata da mazan da a musulunce ya kamata a ce suna dakin miji a kasar nan sai ka rasa ta ina za ka fara. Wato ina nufin sai an yi muhawara kafin a samu matsaya, a ce da ‘yan sakandare za a fara? Ko ‘yan jami’a? Ko ma wanda sam ba su taba yin boko ba? Jama’armu ana cewa cikin maza da mata akwai masu ilimi ko kaji ana aibata mata ‘yan yawon talle ana cewa suke yin bandaro, wato sun girma ba aure ba manemi, yanzu ga maza da mata ‘yan boko wasu ma sun hada biyu ga ilimin addini ga na boko ana ganin su sun makale babu aure, ko har zuwa yaushe za su yi oho! A haka har a tsufa ba a yi aure ba. Mu sani aure fa ibada ne kuma hanyar samun karin natsuwa ne da aure ake tara zuriya, ake more rayuwa ta hanyar debe kewa, ake samun cikar daraja ta mutumtaka da kwarjini da daukaka da kuma lada mai yawa. Har da matasa an masu umarni da su yi aure, yin aure da wuri yana da kyau, kuma iyaye an dora maku hakkin aurar da ‘ya’yanku maza da mata. Ya halatta in ta gagara to kai da kanka ka nema wa diyarka miji, sa’annan magidanta kuma an ce ku kara iyali wato ya zama matanka biyu ko uku ko hudu idan za ku iya yin adalci. To me muke jira ba za mu kara ba? Tabbas duk matar da ke hana mijinta kara aure to

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Mene Ne Dalilinki Na Hana Mijinki ya Kara Aure?
Mene Ne Dalilinki Na Hana Mijinki ya Kara Aure?
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEj3FABgbZt8QWap9UHwvqu45vndzy8ajnqDoQmWAs1LUGCxUwjvdFhCNXmyXB_Y33mfVVqi5gEK1xL_8D4XU5jQ7TogNr4EBwaU-41UxM9EShC9hj6RWjx4tBHHqalOMOWp8nJSSPew3_xh/s320/2018-01-12--01_03_07.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEj3FABgbZt8QWap9UHwvqu45vndzy8ajnqDoQmWAs1LUGCxUwjvdFhCNXmyXB_Y33mfVVqi5gEK1xL_8D4XU5jQ7TogNr4EBwaU-41UxM9EShC9hj6RWjx4tBHHqalOMOWp8nJSSPew3_xh/s72-c/2018-01-12--01_03_07.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2018/11/mene-ne-dalilinki-na-hana-mijinki-ya.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2018/11/mene-ne-dalilinki-na-hana-mijinki-ya.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy