A wannan satin filin yana dauke ne da yadda ake yin Nakiya. Nakiya na cikin kayan gara da Hausawa suke kai wa ‘ya’yansu idan sun yi aure a m...
A wannan satin filin yana dauke ne da yadda ake yin Nakiya. Nakiya na cikin kayan gara da Hausawa suke kai wa ‘ya’yansu idan sun yi aure a matsayin kayan zaki na gara. Don haka makaranta ka da ku ji tsoro ba ina nufin nakiya ta alburushi ba, a a ina nufin nakiya ta ci. Haka ma dakuwa , ba ina nufin zagi ba sai dai dakuwar da ake ci.
*KAYAN DA ZA KI TANADA DON YIN NAKIYA*
1. Shinkafar tuwo
2. Sikari
3. Kanunfari
4. Citta
5. Masoro
6. Barkono
7. Man gyada
*YADDA ZA KI HADA*
Ki sami shinkafar tuwo ki wanke ki shanyata ta bushe, idan ta bushe sai ki zuba a kwarya ki zuba citta da kanunfari da masoro da dan barkono ki kai inji a niko ko kuma idan kina da karfi ki zage ki daka da kan ki har sai tayi gari, ta dakan idan an yi nakiyar tafi gardi, sai dai dakan ne da wuya. Don haka gara ki kai inji a niko miki, idan an niko sai ki saka rariya mai laushi ki tankade sai ki soya garin sama-sama, idan kin gama sai ki shanya ta a tabarma domin ya huce kuma ya dan sha. Sai ki kawo sikarinki ki dafa shi, idan ya dahu sai ki bari ya huce sannan ki zuba shi a cikin wannan garin shinkafar ki ringa juyawa da muciya har sai kin ga ya hade, ki kawo man gyada dan kadan ki zuba ki tuka sosai, sannan sai ki zuba a cikin turmi a kirba har sai kin ga ta kirbu kuma nakiyar ta fara sheki, sai ki kwashe ki cura

COMMENTS