Yakamata magoya bayan jam'iyar APC da munsan muhimcin zabawa shugaba Buhari gwmnoninshi na jam'iyar APC, dominy ta haka ne zai kai m...
Yakamata magoya bayan jam'iyar APC da munsan muhimcin zabawa shugaba Buhari gwmnoninshi na jam'iyar APC, dominy ta haka ne zai kai mataki na gaba cikin kwanciyar hankali, hakika gwamnonin jam'iyar APC da wasu yan takarkarun APC na Arewa da kudu sun taka rawar gani, don ganin nasarar shugaba Buhari, hakika mutane da dama baza su fahimci hakan misali: Mu talakawa munyi zabe, amma akwai tsani da baza mu kai ba, dole wadanan mutane zasu kai. Kamar: A jahar Rivers ministan sufuri da zirga-zirga na Najeriya ya taka rawar gani wajen ganin ba a yi rubutun karya a sakamakon zaben hakan ba. A jahar Kwara ministan yada labarai Lai Muhammad, Gbemi Saraki da Abdulrahaman Abdurazaq sun taka rawar gani, wajen cirewa shugaba Buhari kitse a wuta na kada sanata Bukola Saraki da daukacin mutanensa. A jahar Benue sanata Gorge Akume ya rasa kujerarsa ta sanata don kare muradun shugaba Buhari, ministan gona Audu Obe ya taka rawa a jahar inda shugaba Buhari ya samu kaso 49% na kuri'un da aka kada a jahar Benue. A jahar Akwa ibom sanata Godwin Akpabio ya taka rawar gani a jahar inda ya hana rubutun karya a jahar, kuma yake yunkurin rasa kujerarsa ta sanata saboda kare muradun shugaba Buhari. A Kano gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya yi halacci ga shugaba Buhari inda yakawo kuri'ar da mutane da dama basa tsammani. A jahar Kaduna gwamna Nasir El-rufa'i ya nuna halacci ga shugaba Buhari, duk da bangaranci da kabilanci, da ya shiga siyasar jahar. Haka a jahar Katsina gwamna Aminu Bello Masari ya taka rawar gani tun daga yakin neman zaben shugaba Buhari, har zuwa kawo kuri'a sama da miliyan daya. Jahar Gombe ma Sanata Dan juma Goje da dan takarar gwamnan jahar na jam'iyar APC da sauransu, sun taka rawar gani tunda daga yakin neman zaben shugaba Buhari har ya zuwa zaben. Sai Jahar Niger Wanda banta tunanin Abubakar Lolo zai yi wannan kokari ba sai gasi ya yi. Da sauransu. Don haka idan muka kalli irin wannan dawainiya da wadannan mutane suka yi, dole mu jinjina musu da kuma fitowa ranar Assabar domin kada musu kuri' armu. Daga Sani BelloBature

COMMENTS