Blog Archive

Powered by Blogger.

Dalilin da yasa nake kira a zabi Ganduje – Inji Sheikh Kabiru Gombe

Babban Malamin addinin Musulunci, kuma sakataren kungiyar Jama’atil Izalatil Bidi’a wa Iqamatissunnah, Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana wani k...

Babban Malamin addinin Musulunci, kuma sakataren kungiyar Jama’atil Izalatil Bidi’a wa Iqamatissunnah, Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana wani kwakkwaran dalilin da ya kamata jama’ar jahar Kano su sake zaban Gwamna Abdullahi Ganduje a karo na biyu. Majiyarmu ta ruwaito Kabiru ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da yayi kuma aka nada, da a yanzu haka yake yawo a kafafen sadarwar zamani ana watsa shi, inda yace babban dalilin da zai fada ma Allah idan Ya tambayeshi akan me yace a zabi Ganduje shine Musuluntar da Maguzawa. A jawabin nasa, Shehin Malamin ya bayyana yadda Gwamna Ganduje ya taba gayyatarsu zuwa Musuluntar da wasu maguzawa su dari biyu, da kiristoci guda biyu da suka nuna sha’awar shiga Musulunci. “Allah Ya sani kuka na dinga yi a ranar da muka tafi musuluntar da maguzawan, saboda naga abinda ban taba gani ba, na san irin wahalar da muke sha idan muka shiga garin arna ko maguzawa kafin mu samu mutum 10 sun karbi musulunci, tare da bata tsawon lokaci. Amma sai gashi abin mamaki mutane 202 zasu musulunta a gabana, zasu karbi Kalmar shahada.” Inji shi. Malam Kabiru ya kara da cewa shi da kasan mutane 20 ya baiwa shahada, shima shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau mutane 30 ya baiwa shahada, sai gwamnan jahar Kano daya baiwa kusan mutane 50 shahada, haka nan Shekarau ma ya bada shahada ga mutane 30. Malamin yace haka sauran Maluma suka biyo baya suka yi ta baiwa maguzawanann Kalmar shahada, anayi ana canza musu suna, inda suke zaban sunan daya kwanta musu na Musulunci, har yace a gabansa wani mutumi ya bayyana musu cewa sunansa na yanka Jemage. Daga karshe shehin Malamin ya tabbatar da cewa bayan kammala musuluntar da maguzawan, sai Ganduje ya raba musu kyautar kayan alheri, inda mata suka samu turmin zani da atamfa da jarin kudi, Maza kuma suka samu turmin shadda da jari. ©HausaLoaded

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Dalilin da yasa nake kira a zabi Ganduje – Inji Sheikh Kabiru Gombe
Dalilin da yasa nake kira a zabi Ganduje – Inji Sheikh Kabiru Gombe
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgJwMtZ1eTCyHVRz-unBqOB_z0i7N5hcsZGicaLSPBUHVcnOYe7PBl4CpqDiXWlvrmpGvtu28LnkVFZZkUymEyKvz_dkm_t86lmfmtXLvpo1aAtZsL9XBmHxW_lfrZWn_6lPtDCYw3WlMKc/s320/FB_IMG_1546333451902_2.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgJwMtZ1eTCyHVRz-unBqOB_z0i7N5hcsZGicaLSPBUHVcnOYe7PBl4CpqDiXWlvrmpGvtu28LnkVFZZkUymEyKvz_dkm_t86lmfmtXLvpo1aAtZsL9XBmHxW_lfrZWn_6lPtDCYw3WlMKc/s72-c/FB_IMG_1546333451902_2.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2019/03/dalilin-da-yasa-nake-kira-zabi-ganduje.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2019/03/dalilin-da-yasa-nake-kira-zabi-ganduje.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy