Powered by Blogger.

Wadannan Sune Makiyana a Kannywood inji - Adam a Zango

Fitaccen jarumin Kannywood Adamu Abdullahi Zango ya bayyana ko su waye ya dauka makiya da kuma dalilin da yasa yake musu habaici. A hirar sh...

Fitaccen jarumin Kannywood Adamu Abdullahi Zango ya
bayyana ko su waye ya dauka makiya da kuma dalilin da yasa
yake musu habaici.
A hirar shi da Nasidi Adamu Yahaya, an tambayi Adam Zango
akan dalilin da ya sa yake yawan yi wa makiyansa habaici a
shafukan sada zumunta, sai ya ce yawan makiyan da yake da
su ne ya sa yake yawan wallafa sakon habaice-habaice a
shafinsa na Instagram.
Jarumin ya ce abin da ya dauka makiyi shi ne duk mutumin da
ba ya bukatar ya ga “ci gabanka ko kuma idan ka yi wani abin
burgewa, amma shi bai ga hakan ba, to makiyinka ne.”
“Ko kuma mutumin da idan wani abu ya zo maka na karuwa
kamar karramawa ko taron kalankuwa ko na biki, amma sai ya
ce kar a bai wa wane, gara a bai wa wane, to makiyinka ne.
“Dole ne a masana’antarmu sai ka samu makiya, wasu na
jikinka ne, ko daraktoci, ko jarumai ko furoduoshi ko ‘yan
wasa.
“Dan Adam bai son kishiya, duk wanda ya ga wani yana daga
wa ko yana neman ya wuce shi a daukaka to zai ji haushi,” a
cewar Adamu.
Jarumin ya ci gaba da cewa idan ya yi maganar makiya to ba
da mutum daya ko biyu yake ba, yana magana ne kan mutane
da dama da suke nuna masa irin wadancan halayyar da ya
ambata.
Wanda ya tsargu da shi ake.
Jarumin ya ce idan mutum ya yi habaici to duk wanda ya
tsargu, tabbas yana cikin wadanda ya rubuta sakon saboda su.
“Sannan akwai masu bin mu wato fans, amma kuma makiya
ne.
Za ka yi abin da ba wanda ya taba yi a duniya, amma sai su ce
karya ne kwaikwayon wani ka yi.
“Don haka na kan yi wasu abubuwan ne don na burge
masoyana, a hannu guda kuma na aikewa makiyana sako a
fakaice cewa na san irin kiyayyar da suke min,” in ji Adamu
Zango.
.

COMMENTS

Name

Al'ajabi,13,Android zone,69,Applications,3,Aure,25,Blogger zone,1,computer zone,4,Dadin Kowa sabon salo,27,Facebook zone,12,Free Browsing,2,Hausa Films,1,Hausa novels,1,hotuna,2,Java zone,15,Kannywood,55,kiwon lafiya,35,Mata,12,Musics,24,Network,21,News,146,others,16,siyasa,81,Soyayya,3,Symbian zone,5,Video clips,33,video tutorials,3,Whatsapp,1,
ltr
item
Ameer: Wadannan Sune Makiyana a Kannywood inji - Adam a Zango
Wadannan Sune Makiyana a Kannywood inji - Adam a Zango
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEht0SbT5GxDd5DbkKCY5k9sKJte56KzD_pAPeUTRu9jT2eUgUH7ujS7J6ZjJZTk4DcZEU-VGoZ07LOrwuKzU3l0cBcAcZwTKj4HxYR0Za3E9L9Pb4V4TFb6mLhWG72assUXb35fYJ3Jri5l/s320/Adam-A-Zango-2.jpg
https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEht0SbT5GxDd5DbkKCY5k9sKJte56KzD_pAPeUTRu9jT2eUgUH7ujS7J6ZjJZTk4DcZEU-VGoZ07LOrwuKzU3l0cBcAcZwTKj4HxYR0Za3E9L9Pb4V4TFb6mLhWG72assUXb35fYJ3Jri5l/s72-c/Adam-A-Zango-2.jpg
Ameer
https://ameeryau.blogspot.com/2019/05/wadannan-sune-makiyana-kannywood-inji.html
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/
https://ameeryau.blogspot.com/2019/05/wadannan-sune-makiyana-kannywood-inji.html
true
2994989324915487916
UTF-8
Loaded All Posts Not found any posts VIEW ALL Readmore Reply Cancel reply Delete By Home PAGES POSTS View All RECOMMENDED FOR YOU LABEL ARCHIVE SEARCH ALL POSTS Not found any post match with your request Back Home Sunday Monday Tuesday Wednesday Thursday Friday Saturday Sun Mon Tue Wed Thu Fri Sat January February March April May June July August September October November December Jan Feb Mar Apr May Jun Jul Aug Sep Oct Nov Dec just now 1 minute ago $$1$$ minutes ago 1 hour ago $$1$$ hours ago Yesterday $$1$$ days ago $$1$$ weeks ago more than 5 weeks ago Followers Follow THIS PREMIUM CONTENT IS LOCKED STEP 1: Share to a social network STEP 2: Click the link on your social network Copy All Code Select All Code All codes were copied to your clipboard Can not copy the codes / texts, please press [CTRL]+[C] (or CMD+C with Mac) to copy