Fitaccen jarumin nan na dandalin shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango wanda aka fi sani da Prince Zango ya bayyana dalilin da ...
Fitaccen jarumin nan na dandalin shirya fina-finan
Hausa ta Kannywood, Adam A Zango wanda aka fi
sani da Prince Zango ya bayyana dalilin da ya sa yake
yawan auran mata kuma daga bisani ya rabu da su.
Jarumin ya bayyana cewa ba wai baya iya zama da
mace bane, sai dai
"ba zan iya fada muku abin da ya hada shi da matata
ta farko, da matata ta biyu da kuma matata ta uku ba."
“Allah yana hada mata, mace da namiji. Allah ya
halicci mata domin su kasance ni’ima a garemu maza.
Don mu Allah ya halicce su."
Adam ya kuma bayyana cewa Allah ya rigada ya tsara
ma mutum kaddararsa da abunda zai faru da shi tun
kan a haifasa har izuwa ranar da zai amsa kiran
mahallicinsa.
Dan wasan ya bayyana hakan ne a hira da yayi da
shafin BBC Hausa inda yake cewa:
"Allah Ubangiji ya rubuta wa mutum abin da zai faru
da shi tun daga farkon haihuwarsa har zuwa ranar
mutuwarsa." “Kuma wannan kaddarar da Allah yayi
mun itace tawa, saboda ni , Allah yana gani, Allah ya
ba ni komai da na roke shi, amma ban da mace wanda
nake zaman aure da su.
“Sannan kuma ina so na gayawa mutane wani abu
cewa, duk mutin da ya kasance zai yi aure ya rabu da
mace, ya kara yi kuma ya kara rabuwa da ita, toh ya
kamata su gane cewa wannan mutumin ba mazinaci
ba ne. Saboda ni Adamu Zango Allah ya ba ni, duk
duniya a cikin masana’antar Kannywood, babu wanda
mata ke so iri na. Toh me zan yi da aure?”
©mkntechs

COMMENTS